Abba Ya Dauko Hayar Lauyan Tinubu, Ya Daukaka Kara a Shari’ar Zaben Kano

Abba Ya Dauko Hayar Lauyan Tinubu, Ya Daukaka Kara a Shari’ar Zaben Kano

  • Abba Kabir Yusuf ya samu shigar da kara a babban kotu domin kalubalantar shari’ar zaben Kano
  • Gwamnan jihar Kano da jam'iyyarsa ba su gamsu da nasarar da kotu ta ba Nasiru Yusuf Gawuna ba
  • Lauyan da yake kare Bola Tinubu a kotun zabe, Wole Olanipekun SAN shi ne zai tsayawa NNPP

Kano - Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara domin kalubalantar kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano da ta karbe ikonsa.

Mai girma Abba Kabir Yusuf bai gamsu da hukuncin da aka yi a baya ba, Hasan Sani Tukur ya sanar da cewa gwamnan ya daukaka kara.

Gwamnan jihar Kano ya na fatan a rusa umarnin da kotu ta bada na ba Nasiru Yusuf Gawuna mulki a sakamakon zaftarewa NNPP kuri’u.

Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Siyasar Kano: Shari'ar Abba v Gawuna

Kara karanta wannan

Cikakkun Sunaye: Jerin Jihohin Da PDP, APC da Labour Party Suka Yi Nasara a Kotun Zabe

Abba Yusuf ya shigar da kara mai lamba EPT/KN/GOV/01/2023 ta karkashin jam’iyyar NNPP a ranar 2 ga Oktoba a kotun daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta ce Gwamnan ya roki kotun ta yi sabon hukunci na dabam, ya na zargin alkalan kotun sauraron korafin zabe da sabawa dokar kasa.

Hukuncin Zoom ya saba doka - Abba

Tun farko, Abba Gida Gida kamar yadda aka fi saninsa, ya ce kotun ta sabawa tsarin mulki da ta gabatar da bakon hukunci ta manhajar Zoom.

Lauyan Gwamnan na NNPP ya ce kin zama a zauren kotu domin yin hukuncin ya ci karo da sashe na 36(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Rahoton Premium Times ya ce lauyoyin da su ka daukaka kara su na ikirarin zaftarewa NNPP kuri’u 165,616 ya ci karo da dokokin zabe.

Har ila yau, Gwamnan ya fadawa kotu cewa jam’iyyar APC ba ta gabatar da shaidu daga rumfuna da su ka yi bayani a kan kuri’un da aka soke ba.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

Sannan jam’iyyar NNPP ba ta yarda Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kuri’un da ake bukata daga biyu bisa ukun kananan hukumomin Kano ba.

Mun tuntubi hadimin gwamnan jihar Kano, Hassan Sani Tukur domin jin ta-bakinsa ko su na da kwarin gwiwar nasara a kotun daukaka kara.

Yayin da ake sauraron shari'ar, Legit ba ta iya samun Malam Hassan Sani Tukur ba.

An dauko Wole Olanipekun SAN

Abba ya ce an yi kuskure da aka yi hukunci da takardun zaben da ba a san daga ina su ka fito ba, lauyansa a shari’ar shi ne Wole Olanipekun SAN.

Wole Olanipekun ne ya jagoranci lauyoyin da su ka kare Bola Tinubu a shari’ar zaben shugaban kasa tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi.

Ku na da labari sauran lauyoyin APC sun hada da: Muiz Banire, Ahmed Raji, Akin Olujimi, Yusuf Ali da Lateef Fagbemi wanda ya zama AGF.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng