Lamari Ya Canza, Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Shaidar Tinubu

Lamari Ya Canza, Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Shaidar Tinubu

  • Jami’ar CSU ta amsa tambayoyin da lauyoyin Atiku Abubakar su ke da shi game da Bola Tinubu
  • ‘Dan takaran PDP ya zargi shugaban Najeriya da saba doka ta amfani da takardar karatun bogi
  • Wani ma’aikacin jami’ar ya nuna ba su da masaniya a kan satifiket din da Tinubu ya kai wa INEC

Chicago - Jami’ar CSU da ke kasar Amurka ta ce ba ta dauke da irin takardar shaidar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatarwa INEC.

Caleb Westberg wanda shi ne Magatakardar jami’ar ya shaida haka da yake amsa tambayoyi, Daily Trust ta fitar da rahoton a ranar Laraba.

Kamar yadda Lauyoyin Atiku Abubakar su ka bukata a kotu, an kira jami’in jami’ar ya amsa wasu tambayoyi da za su taimakawa binciken.

Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya na shari'a da Atiku Abubakar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu / officialasiwajubat
Asali: Twitter

An amsa tambayoyin Atiku Abubakar

Kara karanta wannan

Satifiket Din Da Tinubu Ya Bai Wa INEC Na Jabu Ne? Jami'ar Jihar Chicago Ta Bayyana Gaskiya

Ana sa ran ‘dan takaran shugaban kasa na PDP a zaben 2023, zai yi amfani da bayanan a kotun koli inda yake kalubalantar Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya na ikirarin akwai sabani tsakanin takardar shaidar kammala jami’ar da Tinubu ya gabatarwa INEC da asalin na makarantar.

Yayin da yake amsa tambayoyi, Westberg ya ce ba zai iya magana kan takardar da Tinubu ya mikawa INEC ba domin bai taba ganin ta ba.

"Jami'a ta na rike da takardar shaidar da dalibai ba su karba ba ne kurum. Jami’a ba ta ajiye satifiket.
"Ba mu dauke da takardar shaidar da (Bola Ahmed Tinubu) ya gabatarwa Hukumar INEC a hannunmu."

- Caleb Westberg

Jami'ar Amurka ba ta buga sabon satifiket

Da aka yi masa magana a kan abin da ya hana shugaban Najeriya karbar madadin takardar shaidar karatunsa, jami’in ya ce ba su buga sabon satifiket.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan Samun Takardun Bayanan Karatun Tinubu, Atiku Ya Garzaya Kotun Koli

"Ba mu dauke da satifiket din da aka gabatarwa hukumar INEC a hannunmu domin ya riga ya karbe shi."

- Caleb Westberg

Kamar yadda bayanan The Cable su ka nuna, jami’ar ta CSU ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ya na cikin dalibanta, kuma ya kammala karatu a 1979.

Sai dai babu shakka CSU ta yarda akwai sabani wajen ranar haihuwarsa tsakanin 1952 da 1954, jami’ar Amurkan ta ce kuskure aka samu a nan.

Za a tsige Tinubu - Demola Olarewaju

Bangaren Atiku Abubakar su na ikirarin Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa INEC da takardar bogi kamar yadda rahoto ya zo a makon nan.

Dokar kasa ta hana wanda aka samu da takardar shaidar bogi tsayawa takara, Mista Demola Olarewaju ya ce kan haka kotun koli za ta tsige Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng