Tinubu Zai Zama Shugaban Kasan Farko Da Kotun Koli Za ta Tsige, In Ji Hadimin Atiku
- Demola Olarewaju ya huro wuta a kan zargin da ake yi wa Bola Tinubu na amfani da takardar bogi
- Ko da ta tabbata shugaban Najeriya ya yi karatu a jami’ar CSU a Amurka, har yanzu dai bai tsira ba
- Mista Olarewaju ya na zargin wani jabun satifiket ne Tinubu ya yi amfani da shi wajen shiga takara
Lagos - Demola Olarewaju ya na cikin fitattun matasan da ke ba jam’iyyar PDP goyon baya, ya yi magana a kan batun takardar shaidar Bola Tinubu.
Ko da yake tofa albarkacin bakinsa a dandalin X wanda aka fi sani da Twitter, Mista Demola Olarewaju ya yi hasashen samun canjin shugaban kasa.
‘Dan siyasan kuma hadimin Atiku Abubakar ya na ganin cewa kotun koli za ta tsige Bola Ahmed Tinubu, hakan zai ba gwaninsa damar hawa mulki.
Za a cire Tinubu a kotun koli?
A bayanan da ya yi a shafin X a ranar Laraba, ya nuna kusan dole ne Alkalan kotun koli su tunbuke shugaban kasa, ya ce idan ba ayi haka, to da sake.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban farko a Najeriya da za a tsige a kotun koli. Ko dai ayi haka, ko kuwa Najeriya ta tashi aiki – dole ayi dayan biyu."
- Demola Olarewaju
Olarewaju ya ce bayanan da aka samu daga bakin wani ma’aikacin jami’ar CSU a Amurka sun isa hujja wajen kalubalantar Bola Tinubu a kotun koli.
Wani laifi ake zargin Tinubu ya aikata?
A cewarsa, mai girma shugaban kasar ya yi amfani da takardar bogi - dabam da wanda yake fitowa daga hanun jami’a, ya gabatarwa hukumar INEC.
Dokar kasa ta haramta tsaya takarar shugaban kasa ga duk wanda aka samu ya yi karyar takardu, lauyoyin Atiku su na jifan Tinubu da wannan laifi.
"Abu mai sauki. Wannan ya isa Alkalan kotu ta tsige shi ko majalisa ta tunbuke shi. Ko kuma har a daure shi.
Amma ina fatan idan shugaban kasa mai zuwa (idan Allah ya so) ya zo, zai yafe masa, ya yi masa duk wata afuwa."
- Demola Olarewaju
Ba yau aka fara zargin Tinubu ba
Da yake bayani a gidan rediyo, mai ba Atiku Abubakar shawaran a kan dabarun yada labarai, ya kara nanata irin wannan ikirari a gaban duniya.
Rewaju ya shaidawa tashar Splash FM cewa fitaccen lauyan nan, Gani Fawehinmi ya fara bankado zargin da ake yi wa Bola Tinubu a shekarun baya.
Shari'ar zabe a 2023
Ku na da labari Gwamna Mai Mala Buni da AbdulRahman AbdulRasaq sun zarce ba tare da hayaniyar kotu ba, PDP ba ta kalubalanci zabukansu ba.
Haka zalika Isa Liman Kantagi bai yi karar Umar Sani Bago a kotu ba kamar yadda Dikko Radda ya ba Lado Danmarke rata mai yawa - kuri’a 373, 000.
Asali: Legit.ng