Sanatoci Sun Tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio? Gaskiya Ta Fito

Sanatoci Sun Tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio? Gaskiya Ta Fito

  • Wasu rahotanni a soshiyal midiya sun yi iƙirarin cewa an tsige Sanata Godswill Akpabio daga matsayin shugaban majaisar dattawa ta 10
  • Sanata Akpabio, ɗan majaisar tarayya, shi ne shugaban majalisar dattawa na 15 da ke jagorantar majalisa ta 10
  • A binciken da aka gudanar kan batun tsige Sanata Akpabio an gano cewa ba gaskiya bane, ya kamata mutane su guji rahoton da ke yawo

FCT Abuja - Wani faifan bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta Facebook ranar Lahadi ya yi iƙirarin cewa an tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Sanata Akpabio, ya kasance tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma mamban jam'iyyar All Progressive Congress watau APC mai mulkin Najeriya.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Sanatoci Sun Tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio? Gaskiya Ta Fito Hoto: Godswill Abot Akpabio
Asali: Facebook

Ya kama aiki a matsayin shugaban majalisar dattawa a majalisar tarayya ta 10 a wannan shekarar da muke ciki 2023, inda ya gaji Sanata Ahmad Lawal daga jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Wakilin Jihar Kaduna Ya Fadi Ana Kokarin Tantance Sababbin Ministoci a Majalisa

Shin da gaske an tsige Sanata Akpabio?

Rahoton da aka wallafa ya yi iƙirarin cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da Dumi-Ɗum: An tsige shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio daga muƙaminsa saboda ya zama ɗan amshin shatar Tinubu."

Faifan bidiyo ya ja hankalin mutane sama da 171,000 waɗanda suka kalla kuma mutane sama da 1,000 suka yi kwament.

Har zuwa jiya Talata, 3 ga watan Oktoba, 2023, Sanata Akpabio na nan a matsayinsa na mutum lamba ta uku a Najeriya.

Ko a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba, Shugaban majalisar dattawan ya halarci taron addu'o'in godiya na murnar cikar Najeriya shekaru 63 da samun 'yancin kai.

Taron ya samu halartar uwar gidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, Sanata Opeyemi Bami Dele, Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, Ministan Abuja da sauransu.

Rahoton na ƙarya ne

Binciken da muka gudanar ya nuna cewa ba bu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da tsige Akpabio, saboda haka rahoton da ake yaɗa wa na ƙarya ne.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Dauki Nauyin Karatun Dalibai 1498 a Jihar Kano

Philip Shaibu: Mataimakin Gwamnan Edo Ya Shiga Sabon Ofis Tare da Addu'a

A wani labarin kuma Philip Shaibu ya koma sabon ofishinsa na mataimakin gwamna wanda ke wajen gidan gwamnatin jihar Edo.

Mataimakin gwamnan, wanda saɓani da gwamna ya jawo canja masa ofis, ya fara da gudanar da taron addu'o'i a Benin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262