Kotu Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar PDP a Enugu, Ta Ce a Canza Zabe

Kotu Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar PDP a Enugu, Ta Ce a Canza Zabe

  • Jam'iyyar PDP ta ƙara rasa kujerar ɗan majalisa ɗaya a jihar Enugu yayin da Kotun zabe ta bayyana hukuncinta ranar Jumu'a
  • Kwamitin Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Adie Onyebueke, ya rushe zaben inda ya umarci a sake sabo a wasu rumfuna
  • Kotun ta amince da ƙorafin ɗan takarar Labour Party cewa an tafka kura-kurai da saba wa kundin zaɓe a zaɓen ranar 18 ga watan Maris

Jihar Enugu - Kotun sauraron ƙararrakin zaben 'yan majalisar dokokin jiha da na tarayya ta rushe nasarar ɗan majalisar jiha na jam'iyyar PDP a jihar Enugu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Kotun ta soke nasarar Okey Mbah, mamban PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Nkanu ta gabas a majalisar jihar.

Kotun zabe ta yanke hukunci a jihar Enugu.
Kotu Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar PDP a Enugu, Ta Ce a Canza Zabe Hoto: punchng
Asali: Twitter

Haka nan kuma Kotun zaɓen ta umarci hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta shirya sabon zaɓe a wasu rumfuna da aka samu matsala cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Kara karanta wannan

Kujerar Gwamnan PDP Ta Fara Tangal-Tangal, Kotun Zaɓe Zata Yanke Hukunci Kan Zaɓen Da Ya Lashe

Ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, Mista Okwudiri Nnaji, shi ne ya garzaya Kotun yana mai ƙalubalantar matakin INEC na ayyana Mbah a matsayin wanda ya ci zaɓe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai shigar da ƙarar ya yi zargin cewa an yi aringizon ƙuri'u kuma an tafka kura-kuran da suka saɓa wa dokokin zaben Najeriya a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kotu ra raba gardama ranar Jumu'a

A ranar Jumu'a (yau) 29 ga watan Satumba, kwamitin alkalai uku na Ƙotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Adie Onyebueke, ya yanke hukunci kan ƙarar.

A hukuncin, Kotun ta rushe zaɓen kana ta umarci INEC ta shirya sabon zaɓe a wasu rumfunan zaɓe da ke gundumomin Ugbawka da Owo, inda aka soke sakamakon zaɓensu.

Kotun dai ta ce zaben ya yi ƙasa da yadda ake tsammani, tana mai cewa an tafka magudi da rashin bin dokar zabe, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Kwace Ƙarin Kujerar Ɗan Majalisar PDP a Arewa, Ta Bai Wa APC Nasara

Kaduna: Jam'iyyar PDP Ta Yi Watsi da Hukuncin Tabbatar da Nasarar Uba Sani

A wani rahoton na daban Jam'iyyar PDP ba ta gamsu da hukuncin tabbatar da Malam Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna ba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun PDP na jihar ya fitar ranar Jumu'a, ya ce jam'iyyar ta yanke ɗaukaka ƙara zuwa gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262