Ashiru Kudan Zai Daukaka Kara Zuwa Kotun Gaba Don Neman Hakkin 'Yan Jihar Kaduna

Ashiru Kudan Zai Daukaka Kara Zuwa Kotun Gaba Don Neman Hakkin 'Yan Jihar Kaduna

  • Isa Ashiru Kudan, dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a zaben jihar Kaduna ya bayyana matakin da zai dauka
  • Kudan ya bayyana haka ne yayin hira da BBC Hausa a yau Juma'a 29 ga watan Satumba
  • Ya ce wannan gwagwarmaya ta jihar Kaduna ce ba shi kadai ba don haka zai daukaka kara zuwa kotun gaba

Jihar Kaduna - Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan ya ce zai daukaka kara kan shari'ar da aka yi.

A jiya ne kotun sauraran kararrakin zaben jihar ta yanke hukunci inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC, Daily Trust ta tattaro.

Ashiru Kudan ya sha alwashin daukaka kara bayan hukuncin kotun zabe
Ashiru Kudan Zai Dauki Mataki Bayan Hukuncin Kotu. Hoto: Uba Sani, Isa Ashiru Kudan.
Asali: Twitter

Meye Ashiru ya ce kan hukuncin kotu a Kaduna?

Ashiru Kudan na kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani da aka gudanar a watan Maris na farkon wannan shekara.

Kara karanta wannan

Zaben Kaduna: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Gwamna, Ta Fayyace Komai Na Rudani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata hira da BBC Hausa, Ashiru ya bayyana cewa zai daukaka kara don neman hakkin mutanen Kaduna.

Ya ce wannan gwagwarmaya ba ta shi kadai ba ne, ya na wannan ne don jama'ar jihar Kaduna da su ka zaɓe shi.

Ya ce:

"Zan yi kira ga alummarmu su kara hakuri, wannan lamari ya na wurin Allah, kuma a wurinshi mu ke nema da yardar Allah za mu kai ga biyan bukata.
"Wannan hayaniya da ake na kotu ba don kaina na ke yi ba, wannan mu na yi ne don al'ummar jihar Kaduna."

Wane mataki Ashiru zai dauka kan zaben Kaduna?

Ya ce wannan mataki ne na farko, idan lauyoyi su ka ga ba mu gamsu da hukuncin ba za mu daukaka kara zuwa gaba.

Ya kara da cewa tun da akwai rumfunan da aka ce za a sake zabe ai babu maganar janyewa ayi hakuri.

Kara karanta wannan

Kaduna: Isah Ashiru Ya Karyata Uba Sani, Ya Fadi Gaskiyar Hukuncin da Kotu Ta Yanke

Kudan ya ce da wannan yin kanshi ne da ba zai yi ba, amma ya na duba al'ummar jihar Kaduna ne.

Kotu ta tabbatar da Uba Sani a matsayin gwamnan Kaduna

A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben jihar Kaduna ta tabbatar da Uba Sani a matsayin gwamna.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan na kalubalantar zaben gwamnan da aka gudanar a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.