Ogun: Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Jihar a Ranar Asabar
- Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya kusa sanin matsayar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar
- Kotun zaɓen gwamnan jihar ta sanya ranar Asabar, 30 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yanke hukuncinta
- Ɗan takarar PDP, Adebutu na ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a gaban kotun inda ya nemi ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ogun da ke zamanta a Abeokuta, ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam'iiyyar PDP, Ladi Adebutu, ya shigar kan Gwamna Dapo Abiodun.
Jaridar Nigerian Tribune ta kawo rahoto cewa kotun ta bayyana cewa za ta yanke hukuncinta kan shari'ar a ranar Asabar, 30 ga watan Satumban 2023.
Cikin Gwamnan APC Ya Duri Ruwa, Kotu Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Sahihanci Nasararsa a Zabe
Kotun a ranar 4 ga watan Satumba ta tanadi hukuncinta bayan ɓangarorin biyu sun kammala gabatar da bayanansu a gabanta.
Yaushe kotun za ta yanke hukunci?
Rahoton jaridar Daily Trust ya ƙara cewa kotun a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, ta tsayar da ranar Asabar, 30 ga watan Satumba, a matsayin ranar da za ta yanke hukuncinta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sakatariyar kotun, Misis Ezenta Obioma, ta tabbatar da hakan a birnin Abeokuta, babban birnin jihar.
Shi ma Lauyan hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Dakta Remi Olatubora (SAN), ya tabbatar da hakan.
PDP da Adebutu na ƙalubalantar nasarar Abiodun a zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
INEC ta bayyana Abiodun ne a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri’u 276,298, inda Adebutu ya zo na biyu bayan ya samu 262,38 yayin da Biyi Otegbeye na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya zo na uku da ƙuri’u 9,4754.
Meyasa Adebutu ya ƙalubalanci nasarar Abiodun?
Adebutu a cikin karar ya buƙaci kotun ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Masu shigar da ƙarar sun kuma roƙi kotun da ta umurci hukumar zabe ta INEC da ta gudanar da sabon zaɓe a rumfunan zabe 99 da ke gundumomi 41 cikin ƙananan hukumomi 16, waɗanda ko dai ba a gudanar da zaɓe ba, ko kuma aka soke zaɓen saboda hargitsi da aringizon ƙuri'u.
Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Nwifuru
A wani labarin kuma, kotun sauraron koke-koken zaɓen gwamnan jihar Ebonyi ta yi fatali da ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar gwamna Francis Nwifuru.
Kotun ta tabbatar da nasarar da gwamna Nwifuru na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar, 18 ga watan Maris 2023.
Asali: Legit.ng