Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Nasarar Da Atiku Ya Samu Kan Tinubu a Kotun Amurka
- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana ƙoƙarin Atiku Abubakar na ganin kotun Amurka ta umarci CSU da ta saki takardun karatun Shugaba Tinubu a matsayin "ihu bayan hari"
- Jam’iyyar mai mulki ta ce bayanan takardun karatun Tinubu ba zai yi wa Atiku wani amfani ba domin Shugaban ƙasan ba ya da wani abin boyewa
- Wani hadimin shugaban ƙasa ya ce jam’iyyar PDP da Atiku wahalar da kansu kawai suka yi wajen samun bayanan takardun karatun Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja – Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta mayar da martani kan hukuncin da wata kotu a Amurka ta yanke na umartar jami’ar jihar Chicago (CSU) da ta saki takardun bayanan karatun Shugaba Bola Tinubu ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.
Mai Shari'a Tsammani Ya Nemi Yan Najeriya Su Yafe Wa Tinubu Kan Laifin Safarar Kwayoyi? Gaskiya Ta Bayyana
Jaridar The Punch ta rahoto cewa, mataimakin sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Duro Meseko, ya ce ƙoƙarin da Atiku ya yi na ganin an amince da bukatarsa, "ihu ne bayan hari."
Yadda ƙoƙarin Atiku ya zama ihu bayan hari
Meseko ya ce umarnin kotun Amurka bai damu APC ba ko kaɗan, domin Shugaba Tinubu ba ya da wani abin da zai ɓoye.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Shugaban ƙasa ya sha faɗin cewa babu abin da zai boye. Bayanansa suna nan domin kowa ya gani. Jami'ar Chicago kuma ta yi rubuce-rubuce da yawa domin nuna cewa wannan mutumin daga gare mu yake. Babu abin da ya sauya. Babu bukatar ɗaga hankali. Ihu ne kawai bayan hari."
Wani hadimin shugaban ƙasa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Atiku da PDP suna wahalar da kansu ne kawai saboda ba za su iya gabatar da sabbin shaidu a kotun ƙoli ba, waɗanda ba su gabatar ba a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.
A kalamansa:
"Atiku da PDP wahalar da kansu kawai suke. Bayanan karatun shugaban kasa ba su da wata ƙima ga shari’ar Atiku a kotu. A Kotun Koli, ba za su iya gabatar da sabbin shaidu ba waɗanda ba su gabatar ba a gaban kotun shari’ar farko wacce ita ce ƙotun ɗaukaka ƙara da ta yanke hukunci kan ƙarar zaɓen shugaban ƙasa."
Atiku Ya Samu Nasara a Kotu
A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasara a kan Shugaba Tinubu a kotun Amurka.
Kotun Arewacin Illinois ta ƙasar Amurka ta amince da buƙatar da Atiku ya shigar gabanta ta sakin takardun karatun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng