Kwankwaso Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke a Kano

Kwankwaso Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke a Kano

  • Babban jigon jam'iyyar APC a jihar Kano, Dr Ilyasu Musa Kwankwaso, ya yi martani a kan hukuncin kotun zaben gwamna da ta tsige Abba Kabir Yusuf
  • Kwankwaso ya shawarci Abba Gida Gida da ya karbi hukuncin kotu da kyakkyawar zuciya
  • A ranar Laraba, 20 ga watan Satumba ne kotun zaben ta tsige Abba daga kujerar gwamna sannan ta ayyana Dr Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - An shawarci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya karbi hukuncin kotun zaben gwamna da kyakkyawar zuciya, sannan kada ya tunkari kotun daukaka kara ko na koli domin babu kwakkwarar hujja na soke hukuncin kotun zaben.

Tsohon kwamishinan raya karkara, Dr Ilyasu Musa Kwankwaso, ne ya yi wannan martanin jim kadan bayan kotun zaben ta ayyana Dr Gawuna Yusuf, na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zabe, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: NNPP Ta Yi Martani Ga Hukuncin Tsige Abba Gida Gida, Ta Bayyana Yadda Kotun Zabe Ta Yi Wa APC Aiki

An bukaci Abba Kabir Yusuf da ya hakura da zuwa kotun gaba
Kwankwaso Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke a Kano Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

An kuma ayyana Dr Kwankwaso, wanda ya kasance jigo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai bayan kotun zaben ta tabbatar da kararsa kan Dr Yusuf Datti na jam'iyyar New Nigeria People Party (NNPP).

Kwankwaso ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shawarar mai kyau da zan ba Alhaji Yusuf, gwamnan da ya sha kaye, shine kada ya saurari duk wanda ai ba shi shawarar zuwa kotun daukaka kara ko kotun koli."

Nasarar APC nufi ne na Allah, Kwankwaso

Sannan Kwankwaso ya bayyana cewa nasarar da APC ta samu nufi ne na Allah yana mai cewa hujjar da "jam'iyyarmu ta gabatar ya gamsar sosai kuma ya kore duk wani shakku."

Ya ci gaba da cewa:

"Shawarata ga dan uwana, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP shine ya shawarci yaronsa a siyasa Alhaji Abba Yusuf, da kada ya zuba jari wajen zuwa kotun daukaka kara illa ya hada hannu da wanda ya yi nasara a kotun zaben don ciyar da jihar gaba."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban APC Ya Jagoranci Murnar Nasara A Kotun Zaben Kano, Bayanai Sun Fito

Kana da yancin daukaka kara, Kwankwaso ga Abba Gida Gida

Sai dai kuma, ya bayyana cewa koda dai Yusuf na da yancin neman gyara a gaban kotun, ba zai zama daidai ba a gare shi ya ci gaba da bata baitul malin kasar kan manufar da ba za a cimmawa ba.

Ya kara da cewar Kano ta duk dan jihar ne ba tare da la'akari da siyasa ba, yana mai cewa zamanin siyasa ya wuce illa kowa ya hada hannu da Gawuna don samun nasara wajen daukaka jihar.

'Yan kasuwa sun rufe shagunansu a jihar Kano bayan yanke hukuncin kotu

A gefe guda, mun ji cewa sa'o'i kadan bayan sanar da hukuncin kotu, 'yan kasuwa a jihar Kano sun rufe shagunansu zuwa gida.

Kotun ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir tare da tabbatar da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe a jihar, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng