Kotun Sauraran Kararrakin Zabe Ta Kwace Kujerar Kakakin Majalisar Jihar Gombe
- Kotun da ke sauraran kararrakin zabe a jihar Gombe ta rusa zaben kakakin majalisar jihar
- Kakakin majalisar, Abubakar Luggerewo na jam'iyyar APC ya rasa kujerar ta shi ce saboda zargin magudin zabe
- Kotun ta yanke hukuncin ne a yau Talata 19 ga watan Satumba inda ta bai wa Bashir Abdullahi na jam'iyyar PDP nasara
Jihar Gombe - Kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Gombe ta rusa zaben kakakin majalisar jihar.
Kakakin majalisar, Abubakar Luggerewo wanda dan jam'iyyar APC ne na wakiltar mazabar Akko ta Tsakiya a majalisar jihar, cewar Trust Radio.
Wane hukunci kotun ta yanke a Gombe?
Kotun ta yanke hukuncin ne a yau Talata 19 ga watan Satumba inda ta bai wa Bashir Abdullahi na jam'iyyar PDP nasara, cewar Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Michael Ugar ya ce soke zabuka a rumfunan da su ka hada da 001 da 024 da kuma 014 kuskure ne.
Hukumar zabe mai zaman ta soke zaben da aka gudanar a wadannan rumfuna da aka lissafo da ke cikin garin Kumo.
Kotun ta ba da umarnin sake zabe a Kumo ta Tsakiya a rumfar 018 don tabbatar da wanda ya lashe zabe tsakanin Luggerewo da Bashir.
Wasu jama'a sun yi martani ka hukuncin zaben
Ali Kashere ya ce wannan ai ba wani abu ba ne tun da akwai daukaka kara nasara ta Luggerewo ce.
Ya ce:
"Akwai damar daukaka Kara nan da sati biyu kuma tuni Honarabul Luggerewo ya daukaka nan take."
Abdullahi Umar Kumo ana shi martanin ya ce damar Luggerewo aringizon kuri'u ya yi a wancan lokaci.
Musa Sani ya ce ko kadan babu alamun karaya a tare da Luggerewo, mu na fatan nasara.
A cikin kwanakin nan aka nada Luggerewo shugaban kungiyar kakakin majalisu na Arewa maso Gabas, Ripples ta tattaro.
Kotun zabe ta kwace nasarar dan majalisa a Taraba
A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Taraba ta kwace kujerar Nuhu Akila na jam'iyyar PDP.
Kotun bayan kwace kujerar ta tabbatar da nasarar ga dan majalisar APC, Emmanuel George.
Ta kuma umarci hukumar zabe ta dawo da takardar shaidar cin zabe ga George.
Asali: Legit.ng