Kotu Ta Tabbatar Da Lawal Dare A Matsayin Zababben Gwamnan Jihar Zamfara

Kotu Ta Tabbatar Da Lawal Dare A Matsayin Zababben Gwamnan Jihar Zamfara

  • Yayin da ake dakon hukunci kotu kan zaben jihar Zamfara, kotun ta yi hukunci a yau Litinin 18 ga watan Satumba
  • Kotun da ke zamanta a jihar Sokoto ta tabbatar da Lawal Dare a matsayin sahihin zababben gwamna
  • Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle na kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekara

Jihar Zamfara - Kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a jihar Zamfara ta tabbatar da Lawal Dare a matsayin sahihin wanda ya lashe zabe.

Kotun wacce ke zamanta a jihar Sokoto ta yanke hukuncin ne a yau Litinin 18 ga watan Satumba.

Kotu ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin gwamna, ta yi fatali da korafin Matawalle
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Jihar Zamfara. Hoto: @PrettieAdiela, @IsaBature.
Asali: Twitter

Wane hukunci aka yanke tsakanin Dauda da Matawalle?

Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar kuma karamin ministan tsaro a gwamnatin Bola Tinubu ya yi takara a jam'iyyar APC, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya tattaro.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Matashi Ya Lakadawa Kwamishinar Mata Tsinannen Duka Kan Rabon Kayan Tallafi, An Bayyana Dalili

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lawal wanda dan jam'iyyar PDP ne ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekara, Legit ta tattaro.

Yayin yanke hukuncin bayan korar karar, kotun har ila yau, ta ci taran Matawalle Naira dubu 500

Da yake martani, kakakin Gwamna Dauda Lawal, Sulaiman Baba Idris ya ce wannan hukunci ya nuna gaskiyar abin da jama'ar jihar su ka zaba ne.

Meye martanin Gwamna Dauda kan hukuncin ga Matawalle?

Ya ce:

"Wannan ba abin mamaki ba ne, hakan ya nuna gaskiyar abin da mutanen jihar Zamfara su ka goyi baya ne."
"Wannan hukunci zai kara wa Gwamna Dauda Lawal kwarin gwiwar ci gaba da aikin alkairi a jihar da ayyukan ci gaba."

Gwamna Dauda Lawal Dare a zaben da aka gudanar a watan Maris, ya samu zunzurutun kuri'u har 377,726.

Kara karanta wannan

Matawalle vs Dauda: Kotun Zaben Gwamnan Zamfara Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci

Yayin da tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 311,976 inda ya kasance na biyu a zaben.

Kotu za ta yanke hukunci kan zaben jihar Zamfara

A wani labarin, kotun sauraren korafe-korafen zaben jihar Zamfara da ke zamanta a Sokoto ta sa ka ranar Litinin, 18 ga watan Satumban 2023, a matsayin ranar yanke hukunci.

Kotun za ta yanke hukunci ne kan karar da tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya shigar na kalubalantar sahihancin zaben da ya kawo Dauda Lawal a matsayin gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel