Hukuncin Kotu: Jerin Sanatocin Da Za a Gudanar Da Zaben Cike Gurbi a Mazabunsu
FCT, Abuja - Akwai fargaba a tsakanin jam'iyyun siyasa da kuma ƴan Majalisar Dattawa ta 10, a yayin da Kotunan Kararrakin zaɓe a faɗin Najeriya ke cigaba da yanke hukunci.
Legit.ng ta lura cewa an gudanar da zaɓe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, domin zaɓen sanatoci.
Daga hukuncin da kotunan sauraren kararrakin zaben suka yanke zuwa yanzu, aƙalla sanatoci bakwai ne aka soke zabensu. An sallami uku daga cikin sanatocin ne kai tsaye yayin da hudu daga cikinsu za a gudanar da zaɓen cike gurɓi a mazaɓunsu.
Legit.ng ta tattaro muku jerin sunayen sanatoci da za su sake fafatawa a zaɓen cike gurbi.
1) Sanata Thomas Onowakpo, APC, Delta ta Kudu
Kotun sauraren kararrakin zaben ‘yan majalisun tarayya da ke zamanta a garin Asaba na jihar Delta, ta kori Sanata Onowakpo, dan majalisa mai wakiltar Delta ta Kudu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugabar kotun, Mai shari’a Catherine Ogunsola, ta yanke hukuncin janye takardar shaidar cin zaɓen da hukumar INEC ta ba Onowakpo.
Haka kuma ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta gudanar da zaɓen cike gurbi a ƙaramar hukumar Warri ta kudu cikin kwanaki 90.
2) Sanata Ede Dafinone, APC, Delta ta Tsakiya
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya a jihar Delta ta bayyana zaɓen sanatan Delta ta Tsakiya a matsayin wanda bai kammala ba. Hukuncin ya shafi Sanata Dafinone na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Kotun mai alƙalai uku wacce mai shari’a W.I Kpochi ke jagoranta, ya bayar da umarni ga INEC cewa ta sake gudanar da zaɓe a mazaɓu 48 na ƙananan hukumomi huɗu daga cikin takwas na mazaɓar sanatan.
3) Sanata Jibrin Isah Echocho, APC Kogi ta Gabas
Gawuna Ya Yi Magana Kan Nasarar Da Ya Samu a Kotu, Ya Aike Da Sako Mai Muhimmanci Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Sanatan Kogi ta Gabas a ranar Talata 5 ga watan Satumba ta kori Sanata Isah.
An kori Sanata Isah, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da haraji, saboda soke ƙuri’u a wasu rumfunan zaɓe 94 a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
4) Sanata Fred Agbedi, PDP, Bayelsa
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke birnin Yenagoa na jihar Bayelsa ta soke zaɓen Sagbama/Ekeremor tare da ƙwace nasarar Agbedi na jam’iyyar PDP.
Kotun ta kuma umarci INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Abedi cikin gaggawa.
Hukuncin da kotun ta yanke ya ce INEC ta sake gudanar da sabon zaɓe a cikin kwanaki 90 ga wadanda aka hana yin zaɓe a zaɓen ƴan majalisun jihar da ya gabata.
CJN Zai Kafa Kwamitin Alkalan Kotun Koli
A wani labarin kuma, alƙalin alƙalai na Najeriya (CJN) ya shirya kafa kwamitin alƙalan kotun ƙoli da za su saurari ƙararrakin da Peter Obi da Atiku Abubakar suka ɗaukaka kan zaɓen Shugaba Tinubu.
Idan komai ya tafi daidai, a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, alƙalin alƙalan zai sanar da sunayen alƙalan da za su saurari ƙararrakin a kotun ƙoli.
Asali: Legit.ng