Abba Gida Gida Ya Sallami Kwamishinan Da Ya Yi Barazana Ga Alkalan Kotun Zabe

Abba Gida Gida Ya Sallami Kwamishinan Da Ya Yi Barazana Ga Alkalan Kotun Zabe

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kori kwamishinan Safiyo, Adamu Aliyu daga mukaminsa a gwamnatin jihar
  • Adamu Aliyu a jiya Alhamis ya yi barazanar kisa ga alkalan kotun zaben gwamna kan zargin cin hanci
  • Har ila yau, gwamnan ya kuma sallami hadiminsa a bangaren wasanni da matasa, Aliyu Yusuf a mukaminsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kori kwamishinan Safiyo a jihar, Adamu Aliyu daga mukaminsa.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne kan kalaman kwamishinan a jiya inda ya ke barazana ga alkalan kotun zabe.

Abba Kabir ya kori kwamishinan da ya yi barazana ga alkalan kotu
Abba Gida Gida Ya Dauki Mataki Kan Kwamishinan Da Ya Yi Barazana Ga Alkalai. Hoto: Kyusufabba.
Asali: Twitter

Yaushe Abba Gida Gida ya kore shi?

A cikin wata sanarwa, Baba Dantiye, kwamishinan yada labarai a jihar, ya ce Abba Gida Gida ya na mutunta shari’a kuma ba zai bari a ci mutuncinsu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara Sakawa El-Rufai Bayan Nada Yaronshi Shirgegen Mukami, Bayanai Sun Fito

Bayan kwamishinan, Abba Kabir ya kuma kori hadiminsa ta bangaren wasanni da matasa, Aliyu Yusuf, gidan talabijin na Channels ta tattaro.

A jiya Alhamis 14 ga watan Satumba, Adamu Aliyu ya yi barazana ga alkalan kotun zaben jihar kan zargin cin hanci da rashawa.

Kwamishinan ya ce alkalan su zabi rayuwarsu ko kuma kudaden da su ka karba na cin hanci daga sauran 'yan siyasa, cewar Daily Trust.

Ra'ayin wasu kan matakin Abba Kabir a Kano.

Yusuf Muhammad ya ce a cire bambancin siyasa wannan hukuncin gwamnan ya yi dai-dai.

Ya ce:

"Wallahi tunda Abba Kabir yazama Gomnan Kano bai taba burgeni ba irin yau.
"Haka akeson shugabanci, ya barranta gomnatinsa daga kalamansu da kuma sauke su daga mukamansu nan take."

Aisha Sani Ali ta ce:

"Ai wannan hukunci ya zama dole saboda babu yadda za a yi a matsayin shi na mai mukamin siyasa ya fadi wadannan kalamai."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Zai Kashe Naira Biliyan 5 Wajen Gyara Ofishinsa

Mustapha wanda dan jam'iyyar APC ne a Kano ya ce wannan ba shi zai hana Gawuna kwace kujerar ba, da ma ya barsu sun dana.

Meye kwamishinan ke cewa a Kano?

Ya kara da cewa idan su ka ba dai-dai ba bayan yanke hukuncin zabe to komai na iya faruwa a Kano inda ya ce jihar za ta shiga masifa fiye da jihohin Katsina da Kaduna da kuma Zamfara.

Kwamishinan ya bayyana haka a dandazon jama'a da su ka yi dafifi a wurin taron don gabatar da addu'o'i don samun nasara a kotu.

Jam'iyyar adawa ta APC ta shigar da kara kan tafka magudin zaben gwamnan da aka gudanar a watan Maris.

Kwamishina a Kano ya yi barazana ga alkaln kotu

A wani labarin, yayin da ake dakon hukuncin kotun zabe, kwamishinan Safiyo a jihar Kano, Adamu Aliyu ya yi barazana ga alkalan kotun.

Kara karanta wannan

Shugaba Macron Na Faransan Ya Fadi Yadda Sojin Nijar Su Ka Yi Garkuwa Da Jakadansu, Ya Tura Muhimmin Sako

Adamu ya yi wannan barazana ce a jiya Alhamis 14 ga watan Satumba inda ya ce Kano sai tafi jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna shiga masifa.

Ya ce duk wanda bai yi abin da ya dace ba zai iya rasa ransa in dai a kan gwamnatin Abba Kabir ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.