Shugaban Kasa Tinubu Ya Zari Takobin Yaki da Talauci da Rashin Tsaro Har Abada

Shugaban Kasa Tinubu Ya Zari Takobin Yaki da Talauci da Rashin Tsaro Har Abada

  • Bola Ahmed Tinubu ya zauna da shugabannin jihar Ribas a fadar Aso Rock bayan dawowa Najeriya
  • Shugaban kasar ya na ganin babu dalilin da ‘Yan Najeriya za su zauna cikin kangin talauci a yau
  • Mai girma Tinubu yake cewa mutane ba malalata ba ne kuma Ubangiji ya yi wa Najeriya dinbin arziki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A jiya Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin canza halin da ake fama da shi a Najeriya na talauci, rashin tsaro har da rashin cigaba.

This Day ta rahoto Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na mai cewa babu dalilin da Najeriya za ta zauna a cikin wannan mummunan hali.

Mai girma shugaban Najeriyan ya yi maganar da ta zama akasin ta magabacinsa, ya ce al’ummar kasar nan ba malalata ba ne, su na da kokari.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A lokacin mulkinsa, Muhammadu Buhari ya zargi matasa da lalaci a wajen wani taro a waje.

A yayin da ya gana da shugabanni da sauran masu ruwa da tsakin jihar Ribas a fadar Aso Rock, Bola Tinubu ya dauki alwashi zai kawo sauyi.

Kafin ya bar mulki, The Cable ta ce Tinubu ya na so ya ga bayan matsalolin rashin cigaba da su dabaibaye kasar na tsawon shekara da shekaru.

Tinubu yake cewa ya maida hankalinsa wajen ganin yadda ‘yan Najeriya za su samu dukiya.

Tinubu: "Babu dalilin talauci a Najeriya"

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar da jawabi cewa mai gidansa ya fadawa tawagar babu dalilin zama da talauci.

Bai dace mu samu kan mu a yanayin talauci ba. Za mu canza akalar! A cikin tarnanakin nan, akwai inda ya dace mu shiga, za mu gano wurin.

Kara karanta wannan

An Cire Takunkumi: Tinubu Ya Cin Ma Nasarori 3 Daga Zama Da Shugaban UAE

Mu ba malalatan mutane ba ne. Mu na da arziki sosai. Mu na bukatar kurum mu zama ‘yan uwan juna ne kuma mu rufawa juna asiri.

Bola Tinubu ba zai tsaya bada uzuri ba

Ni ba shugaban kasar da zai rika bada uzuri ba ne. Zan yi bakin kokari domin kasarmu ta samu manufa, ta jajirce, kuma a samu arziki.
Babu dalilin da za mu yi talauci! Ba za mu waiga baya ba, kuma za mu tafi gaba da karfi.

- Bola Tinubu

An yabawa shugaba Tinubu

Kwanaki labari ya zo cewa Bola Tinubu ya ce a fitar da kudi a biya iyalan sojojin da su ka rasu wajen yaki, ya kuma bukaci a magance rashin tsaro.

Shugaban hafsun sojojin kasa, Janar Taoreed Lagbaja ya yi wannan bayani a wajen bude babban taron sojoji na shekarar nan da ake yi a garin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng