Rikicin Wike Da PDP: An Bayyana Abin Da Zai Faru Idan PDP Ba Ta Yi Taka Tsan-Tsan Ba

Rikicin Wike Da PDP: An Bayyana Abin Da Zai Faru Idan PDP Ba Ta Yi Taka Tsan-Tsan Ba

  • Har yanzu rikicin da ke tsakanin Wike da jiga-jigan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cigaba da ɗaukar zafi
  • A cikin ƴan kwanakin nan tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi kiran da a dakatar da Atiku Abubakar wanda hakan ya sanya ya sha caccaka
  • Da yake magana da Legit, wani mai sharhi kan lamuran siyasa, Segun Akinleye, ya ce lokacin da PDP za ta zaɓi korar Wike, babu wanda zai tausaya masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wani mai sharhi kan lamuran siyasa, Segun Akinleye, ya bayyana cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike na barazanar lalata jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Akinleye, a wata tattaunawa da Legit, ya yi nuni da rikicin shugabancin jam'iyyar Labour Party (LP’s), inda Julius Abure da Lamidi Apapa, ke ayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar na ƙasa.

Kara karanta wannan

Wole Soyinka Ya Tonawa Obidient Asiri, Sun San Peter Obi Bai Doke Tinubu ba

Mai sharhi ya yi magana kan rikicin PDP da Wike
Wike na cigaba da caccakar PDP Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

"Ba wanda zai tausaya wa Wike": Mai sharhi

A cewar Akinleye, lokacin da jam'iyyar PDP ta yanke shawarar hukunta Wike, babu wanda zai tausayawa ministan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Idan PDP ba ta yi taka tsan-tsan ba, Wike a shirye yake ya mayar da jam'iyyar abin da Labour Party ta ke fuskanta a wajen Lamidi Apapa da Julius Abure.
"Za ka iya yarda cewa jam'iyyar ta shirya ɗaukar mataki, sannan lokacin da za ta yi hukuncin, babu wanda zai tausaya wa Wike."

Dalilin da yasa PDP ba ta hukunta Wike ba

Akinleye ya bayyana cewa PDP ba ta dakatar da Wike ba ne saboda umarnin kotu da ta hana jam'iyyar dakatar da shi

A na shi ɓangaren kuma ministan na Abuja, ya ƙi daina takalar PDP da Atiku Abubakar faɗa. Sai dai, jam'iyyar ba ta dakatar da shi ba.

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Wike Ke Son Kawo Ruɗani a Jam'iyyar PDP

PDP Ta Samu Rauni a Jihar Kogi

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gamu da cikas a jihar Kogi, yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar.

Hakan ya auku ne bayan tsohon matiwamnan jihar Kogi, Arc Yomi Awoniyi, ya tabbatar da koma wa jam'iyyar APC a hukumance gabanin zaɓen gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng