Rigima ba ta Kare ba, NNPP da Kwankwaso Za Su Gwabza a Kan Tambarin Jam’iyya
- Wasu jagororin NNPP sun nuna babu ruwansu da kokarin da ake yi a canza tambarin jam’iyya
- Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa su na shirin kawo canza a kundin tsarin mulkin NNPP
- Peter Ogah ya sanar da hukumar INEC cewa wadanda su ka kafa jam’iyya ba su san da batun ba
Abuja - Jam’iyyar NNPP ta rubutawa hukumar INEC takarda a game da shirin da wasu su ke yi na canza tambarin da aka san ta da shi.
Vanguard ta kawo rahoto dazu cewa Peter Ogah ya rubuta wasika a madadin jam’iyyar wanda ta shiga hannun manema labarai a Legas.
Haka kuma jam’iyyar adawar ta kuma aika takarda zuwa ga Rabiu Musa Kwankwaso domin a janye yarjejeniyar da aka yi da Kwankwasiyya.
Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce Mista Peter Ogah ya zargi wasu marasa hurumi da neman canza masu tambari da tsarin mulki.
Kwankwaso ba su da hurumi a NNPP?
"Mu ne lauyoyin jam’iyyar NNPP, ta karkashin Dr Boniface Okechukwu Aniebonam wanda ya kafa ta da shugaban BOT, Dr Temitope Aluko, mu na rubuto wannan bisa umarninsu
Wadanda mu ke karewa a gaban shari’a sun ce wasu daidaikun mutane su na yunkurin canza tambarin jam’iyya kuma su canza doka, saboda haka dole mu fito da wannan sanarwa.
Ana sanar da hukumar a doka cewa wasu da ba su da iko su na wannan mugun tsari, saboda haka dole ayi watsi da wannan ko kuma ka da a saurari wanin canji da bai fito daga jam’iyya ba."
- Peter Ogah
The Nation ta ce Ogah a wasikarsa ya yi godiya ga hukumar INEC bisa bin dokar kasa da ta ke yi.
Yarjejeniyar Kwankwasiyya da NNPP
A game da ‘dan takaran shugaban kasa na 2023, takardar ta tuna masa yarjejeniyar da aka yi a Fabrairun 2022 tsakanin Kwankwasiyya da NNPP.
A cewar Ogah, jagororin NNPP sun godewa mabiya Kwankwasiyya da su ka hada-kai da su a zaben 2023, su ka ce yanzu Allah ya raka taki gona.
Yadda za a gyara zaben Najeriya
A ra’ayin Osita Chidoka, an ji ya na cewa bai dace a rika shari’ar sauraron karar zabe bayan an yi rantsuwa ba saboda ba za ayi adalci a kotu ba.
‘Dan siyasar ya na so a wajabta samun goyon bayan 50% a zabe kafin ‘dan takara ya karbi mulki, hakan zai kara farin jini da karbuwar shugaba.
Asali: Legit.ng