Atiku Abubakar Ya Yi Jimamin Rasuwar Sama Da Mutane 10 a Hadarin Jirgin Ruwa a Adamawa

Atiku Abubakar Ya Yi Jimamin Rasuwar Sama Da Mutane 10 a Hadarin Jirgin Ruwa a Adamawa

  • Dan takarar shugabancin ƙasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna alhininsa kan haɗurran jiragen ruwa a Adamawa
  • Atikun ya koka kan yawaitar haɗurran jirgin ruwan da ake samu a sassa daban-daban na Najeriya
  • Ya yi kira ga gwamnati da ta tashi tsaye wajen inganta harkokin sufurin ruwa don kare rayuka da dukiyoyin al'umma

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna alhininsa bisa haɗurran jirgin ruwan da suka janyo sanadin mutuwar mutane sama da 10 a jihar Adamawa.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, 12 ga watan Satumba.

Atiku ya yi jimamin rasuwar mutane a haɗarin jirgin ruwa
Atiku ya yi jimamin rasuwar mutane a haɗurran jiragen ruwa. Hoto: Atiku Abubakar/Facebook, Vanguard
Asali: UGC

Atiku ya yi jimamin mutuwar mutane sanadiyyar hadarin jirgin ruwa

Atiku ya ce ya yi matukar damuwa da mutane sama da 10 da suka rasa rayukansu a haɗarin jirgin ruwan da ya afku a ƙauyen Gurin da ke ƙaramar hukumar Fufore ta jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Kan Haɗurran Jiragen Ruwan da Suka Faru a Jihohin Arewa 2

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan ya kuma nuna alhininsa bisa wani haɗarin da ya faru a Rungange da ke ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a ƙarshen makon da ya gabata.

A kalamansa:

“Na yi bakin ciki da jin labarin kifewar Wani jirgin ruwa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 10 tare da bacewar wasu da dama a kauyen Gurin Dake karamar hukumar Fufore, Kuma Hakan na faruwa ne kasa da sa'o'i 48 da faruwar makamancin hadarin a Rungange Dake karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.”

Atiku ya ba da shawarar yadda za a magance haɗurran jirgin ruwa

Atiku Abubakar ya kuma koka kan yadda ake yawaitar samun haɗurran jiragen ruwa a sassa daban-daban na Najeriya, wanda kan janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Atiku ya nemi gwamnati da ta yi hoɓɓasa wajen inganta hanyoyin sufurin jiragin ruwa, ta yadda za a magance matsalolin da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Neman Dawowa Ɗanye, Tsagin Atiku Ya Maida Martani Mai Zafi Ga Wike

Wani ɓangare na kalaman na sa na cewa:

“Wadannan munanan hadarurruka na ci gaba da zama abin damuwa mutuka, duba da yadda abin ke faruwa akai-akai a baya-bayan Nan. Daga jihar Neja, Jihar Kwara sai Adamawa da yankin Neja-Delta.”
“Wadannan hadarurruka na jaddada bukatar gwamnati ta Bada kulawa ta musamman a fannin zirga-zirga ta hanyoyin ruwa, domin saukakawa Jama'a tare da bunkasa tattalin arziki da kuma kare aukuwar hadarin kifewar jirage.”
“Ya kamata hukumomin da abin ya Shafa su dauki matakan da suka dace domin rage aukuwar irin wadannan hadarurruka.”

Mutane sama da 10,000 sun ɓata a ambaliyar ruwa a Libya

Legit Hausa ta yi rahoto a baya kan ambaliyar ruwan da ta janyo ɓacewar sama da mutane 10,000 a yankin Derna da ke gabashin ƙasar Libya.

An bayyana cewa sama da gawarwakin mutane 1,000 aka yi nasarar ganowa ya zuwa yammacin ranar Talata 12 ga watan Satumban da muke ciki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rayukan Mutane Da Dama Sun Salwanta a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa a Arewacin Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng