Mu ba Sakarkaru ba ne: Abin da Ya sa Wike Yake Son Karya Atiku da PDP - 'Dan PCC
- Nyesom Wike ya na ganin bai kamata a cigaba da zama da su Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP ba
- Wannan ya tsokanowa Ministan na Abuja martani daga wani ‘dan majalisar PCC, Pedro Obaseki
- Ba komai ya jawo Wike ya ke son ganin bayan Atiku Abubakar ba face takarar 2027 inji ‘dan siyasar
Abuja - Petro Obaseki ya na cikin jagororin a jam’iyyar PDP a kudancin Najeriya, ya maida martani ga wasu kalaman Nyesom Wike.
Punch ta ce Mista Pedro Obaseki ya zargi ministan birnin tarayya na Abuja, Nyesom Wike da neman karya jam’iyyar hamayya ta PDP.
‘Dan siyasar ya ce ba komai ya sa tsohon gwamnan ya ke haka ba illa domin ya samu takarar shugaban kasa cikin ruwan sanyi a 2027.
Obaseki: "Wanene Nyesom Wike a PDP?"
Obaseki wanda ya na cikin ‘yan kwamitin PDP na yakin zaben shugaan kasa a 2023 ya ce Wike ba kowa ba ne idan ana maganar jam’iyya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Obaseki, ministan ya yi amfani da wasu jiga-jigan jam’iyyarsu ta PDP ne ya samu mukamai, daga nan kuma sai ya ci amanarsu.
Na kusa da Atiku Abubakar din ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da wasu manema labarai, ya na mai raddi ga ministan kasar.
Za a kori Atiku daga jam'iyyar PDP?
Rahoton Daily Trust ya ce hakan ya biyo bayan kiran da ak aji Wike ya yi na cewa a dakatar da Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal daga PDP.
A nan ne jagoran jam’iyyar ta PDP yake cewa lamarin tsohon gwamnan Ribas ya fara yawa.
"Ba boyayyen abu ba ne cewa abin da Wike yake sha’awa kurum shi ne zama shugaban kasarmu
Duk abin da zai tare masa hanya wajen cin ma wannan, zai yi shi kuma abin da yake yi kenan.
Abin da mu ke gani yanzu shi ne ya na fada ne domin ya karya PDP, ta yadda zai karya APC domin ya nemawa kansa hanyar takara a 2027
Amma mu ba sakarkaru ba ne. ya na da muhimmanci mu ja-kunnen Wike. Akwai iyakar mutumin da ya kamata ya yi wa Ubangiji godiya."
- Pedro Obaseki
A cewar Obaseki, Wike ya ci amanar Rotimi Amaechi, Goodluck Jonathan, Peter Odili, da Atiku Abubakar, yanzu ya koma wajen Bola Tinubu.
Bola Tinubu a G20
Ku na da rahoto cewa nan da wani lokaci kadan mutane za su san muhimmancin ziyarar Shugaban Najeriya zuwa kasar Indiya wajen taron G20.
Ana sa ran zuwan Bola Tinubu kasar wajen zai inganta tsaro da tattalin arziki, tare da jawo 'yan kasuwar Indiya za su sa hannun jari a Najeriya.
Asali: Legit.ng