Jigon APC Ya Bukaci Atiku, Peter Obi Su Hada Hannu Da Shugaba Tinubu

Jigon APC Ya Bukaci Atiku, Peter Obi Su Hada Hannu Da Shugaba Tinubu

  • Kotun zaɓe ta tabbatar da zaɓen Bola Tinubu sannan ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Kotun ta kuma yi fatali da ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar Tinubu waɗanda Atiku da Peter Obi suka shigar
  • Da yake martani kan hakan, jigon APC a jihar Plateau, Mr. Williams Dakwom, ya yaba da hukuncin kotun sannan ya buƙaci Atiku da Obi su goyi bayan gwamnatin Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mista Williams Dakwom, mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar Plateau, ya yaba da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke.

Legit.ng ta rahoto cewa kotun a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba ta yi fatali da ƙararrakin Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party, kan nasarar shugaban ƙasa Tinubu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

"Peter Obi Ya Kusa Zama Shugaban Kasa": Babbar Malamar Addini Ta Fadi Wani Sabon Wahayi

Jigon APC ya bukaci Atiku, Obi marawa Tinubu baya
Jigon APC Ya bukaci Atiku, Peter Obi su hada hannu da gwamnatin Shugaba Tinubu Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Da yake martani, Mista Dakwom a wata tattaunawa da Legit.ng a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, ya bayyana cewa hukuncin kotun ya tabbatar da nasarar da ƴan Najeriya suka ba Tinubu a lokacin zaɓen.

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Maganar gaskiya wannan zaɓen 2023 yana da damar zama wanda ya fi kowanne zaɓe kammaluwa cikin nasara a tarihi, amma abun takaici ƴan Obidients/Atikulated sun yi amfani da farfaganda wajen kawo ruɗani."
"Duk da haka, ko ɗan takarar da ya yi nasara bai samu ƙuri'u miliyan takwas ba. Muna godiya ga alƙalan kan yadda suka yi bayanin gaskiya. Abin da mu ke addu'a shi ne Allah ya taimaki shugaban ƙasar mu ya iya aiwatar da ayyukan da ya shirya yi wa ƙasar nan."

Jigon APC ya aike da saƙo mai muhimmanci ga Atiku, Peter Obi

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Atiku Da Peter Obi Sun Bayyana Matakin da Zasu Ɗauka Bayan Ƙotun Zabe Ta Yanke Hukunci

Da yake cigaba da magana, Dakwom, ya buƙaci ƴan takarar shugaban ƙasar da su amince da hukuncin kotun sanann su marawa gwamnatin Shugaba Tinubu baya domin cigaban ƙasar nan.

"Yakamata su yi biyayya ga hukuncin kotun, su ajiye girman kai gefe guda sannan su amince da shi. Su zo su haɗa hannu da shugaban ƙasa domin ciyar da ƙasar nan gaba." A cewarsa.

Tinubu Zai Cigaba Da Nasara Kan Atiku, Obi - Hamzat

A wani labarin na daban kuma, shugaban Connected Development (CODE) Hamzat Lawal ya yi tsokaci kan hukuncin kotun zaɓen shugaban ƙasa.

Hamzat ya bayyana cewa idan har ba haɗaka Atiku da Peter Obi suka yi ba, ba za su iya yin nasara akan Shugaba Tinubu ba a zaɓen 2027 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel