Kwankwaso Ya Fara Shirin Canja Tambarin NNPP Da Gyara Dokokin Jam'iyyar

Kwankwaso Ya Fara Shirin Canja Tambarin NNPP Da Gyara Dokokin Jam'iyyar

  • Rigimar da ta tsaga jam'iyyar NNPP gida biyu ta ɗauki sabon salo yayin da tsagin Kwankwaso ya fara ɗaukar matakai masu tsauri
  • Bangaren da ke goyon bayan Kwankwaso ya fara yunkurin sauya tambari da kundin dokokin jam'iyyar NNPP gaba ɗaya
  • Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan tsagin Agbo ya kori tsohon gwamnan Kano din daga NNPP

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rikicin da ke neman tarwatsa jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya ɗauki sabon salo yayin da tsagin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya fara shirin sake fasalin jam'iyyar.

Jaridar Punch ta ce tsagin NNPP mai goyon bayan Kwankwaso sun fara yunkurin sauya tambarin jam'iyyar da kuma garambawul ga kundin mulkin NNPP.

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso Ya Fara Shirin Canja Tambarin NNPP da Gyara Dokokin Jam'iyyar Hoto: KwankwasoRM
Asali: UGC

An tabbatar da matakin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin ne yayin wata tattaunawa ta musamman da babban mai binciken kudi na NNPP, Ladipo Johnson.

Kara karanta wannan

Al’ummar Yarbawa Sun Yi Wa Kwankwaso Da Gwamnatin Kano Addu’a Ta Musamman

Wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki uku bayan tsagin Major Agbo sun kori ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP daga jam'iyyar bisa zargin cin amana da sace kuɗin kamfe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matakin korar Kwankwaso na ƙunshe a wata sanarwa da ta fito ranar Talata ta hannun Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar NNPP, Abdulsalam Abdulrasaq, Vanguard ta rahoto.

Abdulrasaq ya tabbatar da cewa an dauki matakin korar Kwankwaso nan take bayan ya gaza gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa don kare kansa kan zargin da ake masa.

Tsagin Kwankwaso sun yunƙuro

Kwanaki kadan bayan wannan dirama, Punch ta gano cewa akwai wani shiri da tsagin Kwankwaso ya yi na gyara tambari da kundin dokokin jam'iyyar da nufin rage ƙarfin wanda ya kafa NNPP, Boniface Aniebonam.

Da aka tambaye shi, ko suna shirya wannan gyaran ne domin maida martani ga sabon tsagin NNPP da ya ɓullo, Johnson ya ce:

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Tsoma Baki a Rigimar Jam'iyyar APC Da Korar Jiga-Jigai 84

"Aa, wannan matakin ba shi da alaƙa da ɗaya tsagin, abu ne da muka tattauna a taron NEC. Ba kamar su ba (tsagin Agbo) mu dagaske muke. Amma ba mu kai da sauya tambari ba, muna shirin ba mambobin mu dama."

Da yake martani, mukaddashin shugaban jam'iyyar, Manjo Agbo, ya shaida wa wakilinmu cewa, suna sane da matakin da suke ganin an dauka domin durƙusar da wanda ya kafa NNPP.

Mubarak Lado, jigon NNPP kuma ɗan Kwankwasiyya a Katsina ya shaida wa Legit Hausa cewa duk matakin da mai gida ya ɗauka suna goyon bayansa 100 bisa 100.

Ya ce:

"Naji daɗin wannan labarin kuma mu dama don Kwankwaso muka shigo jam'iyyar NNPP, idan ya fita kafarmu kafarsa, idan kuma ya zauna muna tare da shi."
"Rikicin da ke faruwa yana buƙatar a zauna a sake sabon lale, saboda haka muna tare da wannan yunkurin, Allah ya taimake su amma ka san mu an ce an dakatar da mu, Katsina da wasu jihohi."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Wurin Ibada a Jihar Kaduna, Sun Kashe Malami

Gwamnatin Tinubu Zata Gina Gidaje 7,000 a Wasu Jihohin Arewacin Najeriya

A wani labarin kuma Gwamnatin Bola Tinubu za ta gina gidaje 1000 a kowace jiha daga cikin jihohi 7 da rashin tsaro ya addaba a arewacin Najeriya.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce shugaba Tinubu ya ware makudan kudaɗe don warware matsalar 'yan arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262