Adamawa: Abinda Ya Sa Muka Sa Hoton Gwamna a Buhunan Shinkafa. Hadimi
- Gwamnatin jihar Adamawa ta yi ƙarin haske kan dalilin sanya hoton gwamna Fintiri a jikin buhunan Shinkafar tallafi
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tura wa jihohi kuɗi da kayan abinci domin raba wa yan Najeriya su rage radaɗin cire tallafin fetur
- Shugaban ma'aikatan gwamna Ahmadu Fintiri ya ce sun manna hoton ne domin hana cinikin kayan a baƙar kasuwa
Jihar Adamawa - Shugaban ma’aikatan gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, Edgar Amos, ya kare matakin sanya hoton gwamnan a jikin buhunan shinkafa da aka raba wa jama’a a matsayin kayan agaji.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sakamakon wahalhalun da aka shiga bayan cire tallafin man fetur, gwamnatin tarayya ta saki kudi da kayan abinci ga jihohi a raba wa talakawa.
Gwamnonin dai sun yi ta rabon kayayyakin tare da raba kudade ga mazauna jihohinsu, duk da cewa an yi ta cece-kuce kan daraja da ƙimar kayayyakin da ake bayarwa.
Dalilin sanya Hoton Fintiri - Amos
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, Amos ya ce an ɗora hoton gwamnan a buhunan shinkafa ne domin tabbatar da cewa ba a karkatar da kayan abincin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton jaridar Pulse, Mista Amos ya ce:
"Wannan wani sabon abun cece-kuce ne ga wasu, amma duk da haka muna sanya Hoton shugaba Tinubu a dukkan ofisoshin kasar nan, ko ka zaɓe shi ko baka zaɓe shi ba, shi ne shugaban Najeriya."
"Nan kuma shi ne gwamnan Adamawa, ko kun zabe shi ko ba ku zabe shi ba, kuna da hotunansa a ofisoshi, don haka yana da fa'ida, hakan na nufin mai son ya je kasuwa ya sayar da tallafin ba zai iya ba saboda an yi masa alama."
“Kuma wannan shi ne gwamnan da jama’a ke so, mutun yaga hoton wanda yake so kuma ya ci shinkafar cikin buhun, haka abin yake. Wa kuke tsammanin zamu sa Hotonsa a alal misali?"
Ya ƙara da cewa duk talakan da ke kukan yunwa kuma ya tsaya yana gardama kan me zai sa a sanya Hoton gwamnan to lallai ba yunwa yake ji ba.
Fintiri Ya Ce Zai Rushe Duk Gidan Da Aka Samu Dauke Da Kayan Abincin Da Aka Wawuso Daga Ma'ajiya
A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya buƙaci waɗanda suka saci kayayyakin abinci su dawo da su cikin ruwan sanyi.
Ya bayyana hakan ne a Yola biyo bayan wawushe kayayyakin abinci da aka yi daga rumbun ajiyar jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng