Jerin Sunayen Mata Mataimakan Gwamnonin Jihohi 8 A Najeriya
Yayin da mata ke yawan korafi na rashin saka su a harkokin siyasa, da alamu ba na sun fara samun biyan bukata.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yawan mata a harkokin siyasa da kuma mukamai kullum karuwa ya ke a Najeriya.
Zaben 2023 ya zo da sabon salo ganin yadda mafi yawan 'yan siyasa su ka jawo mata a jiki.
Legit.ng Hausa ta jero muku mata mataimakan gwamnoni a jihohinsu:
1. Noimot Salako-Oyedele -Jihar Ogun
Noimot ta kasance mataimakiyar gwamnan jihar Ogun tun 2019 karkashin mulkin APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An haifi Injiniya Noimot Salako-Oyedele a watan Janairu 1966 a Ota da ke karamar hukumar Ado-Odo/Ota da ke jihar, The Nation ta tattaro.
Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke, Ya Fada Wa Atiku da Obi Mafita
2. Akon Eyakenyi - Jihar Akwa Ibom
An haifi Eyakenyi a ranar 28 ga watan Nuwamba 1965 a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa.
Sanata Eyakenyi ta wakilci Akwa Ibom ta Kudu daga 2019 zuwa 2023 kafin nada ta wannan mukami.
3. Kaletapwa George Farauta - Jihar Adamawa
An haifi Farauta a ranar 28 ga watan Nuwamba a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa.
Farauta malamar jami'a ce kuma 'yar siyasa wacce ta rike kwamishinan ilimi mai zurfi da kuma shugabar hukumar ilimi daga tushe (ADSUBEB) ta jihar.
4. Hadiza Sabuwa Balarabe - Jihar Kaduna
An haifi Hadiza a ranar 28 ga watan Agusta 1966, ta kasance mace ta farko da ta samu wannan mukami a Arewa maso Yamma.
Ta fito daga karamar hukumar Sanga ta jihar inda ta yi wa tsohon gwamna Nasiru El-Rufai mataimakiya kafin a sake zabanta a 2023.
5. Monisade Christiana Afuye - Jihar Ekiti
An haifi Afuye a ranar 28 ga watan Satumba 1958 a Ikere Ekiti da ke jihar.
Ta rike shugabar matan APC na jihar, ta na da 'ya'ya da kuma jikoki.
6. Josephine Chundung Piyo - Jihar Plateau
Piyo tsohuwar 'yar majalisa ce a jihar a 1999, ta kuma rike hadimar gwamnan jihar daga 2008 zuwa 2012.
An zabe ta mataimakiyar gwamnan jihar a 2023 karkashin jam'iyyar PDP.
7. Ngozi Nma Odu - Jihar Rivers
An haifi Odu a ranar 23 ga watan Oktoba 1952 a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni da ke jihar.
An zabe ta a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar a 2023 karkashin jam'iyyar PDP.
8. Patricia Obila - Jihar Ebonyi
An haifi Obila a ranar 12 ga watan Yuni 1975 a Abakaliki da ke jihar Ebonyi.
Ta samu nasarar lashen zaben 'yar majalisa a 2023 sannan ita ce farkon mace da ta taba rike mukamin a jihar.
Ariwoola, Abba Aji Da Sauran Alkalan Kotun Koli Da Za Su Yanke Hukunci
A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke hukunci a Abuja.
'Yan takarar shugaban kasa a jam'iyyun adawa za su daukaka kara don kalubalantar hukuncin.
Asali: Legit.ng