Jam'iyyar Labour Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe

Jam'iyyar Labour Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe

  • Jam'iyyar Labour, ta ɗan takarar shugabancin ƙasa Peter Obi, ta yi watsi da hukuncin kotun zaɓe
  • A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba ne dai kotun zaɓen ta yi watsi da mafi yawa daga Korafe-korafen da jam'iyyar ta shigar
  • Jam'iyyar ta Labour ta bayyana cewa za ta sanar da matakin da za ta ɗauka nan ba da jimawa ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam'iyyar Labour, wato jam'iyyar ɗan takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ta ce bata amince da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ba.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Obiora Ifoh ne ya bayyana matsayin jam’iyyar, jim kaɗan bayan bayyana hukuncin kotun a Abuja kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A zaman kotun sauraron ƙararrakin zaɓen na ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, ta yi watsi da mafi yawa daga Korafe-korafen da Peter Obi da jam'iyyar Labour suka shigar.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Babban Sanatan Jam'iyyar APC, Ta Bayyana Dalilanta

Jam'iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe
Jam'iyyar Labour ta su Peter Obi, ba ta amince da hukuncin kotu ba, za ta sanar da mataki na gaba. Hoto: Kola Sulaimon/AFP
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar Labour ta ce bata amince da hukuncin kotun zaɓe ba

Obiora ya bayyana cewa hukuncin da alƙalai biyar na kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka yanke ya saɓa da abinda 'yan Najeriya ke tsammani kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa 'yan Najeriya sun shaida yadda aka yi mu su fashin zaɓe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, wanda duk duniya ta yi Allah wadai da shi, amma sai ga shi kotu ta aminta da zaɓen.

Ya jinjinawa lauyoyinsu bisa jajircewarsu, inda ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da hawan ƙawarar da a cewarsa aka yi wa dimokuraɗiyya.

Jam'iyyar Labour za ta sanar da mataki na gaba

Obiora Ifoh ya bayyana cewa ba za su bari dimokuraɗiyya ta gaza a Najeriya ba, za su ci gaba da ganin an tabbatar da ita.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Malamin Addini Ya Fadawa Alkalai Abinda Ya Kamata Su Yi

Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar ta Labour party za ta bayyana matsayarta bayan tattaunawa da lauyoyin da ke kareta a gaban shari'a.

Daga ƙarshe ya yi kira ga magoya bayan dimokuraɗiyya kan su ƙara ƙaimi gami da sanya kyakkyawan fata a cikin ransu cewa, watarana al'amuran Najeriya za su daidaita.

Kotu ta karɓe kujerar sanatan APC ta bai wa na PDP

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kujerar sanatan da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sadiku-Ohere da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke Lokoja ta karɓe a yayin zaman da ta yi ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Kotun ta hannanta kujerar sanatan ga Natasha Akpoti ta jam'iyyar PDP, wacce ita ce aka tabbatar da ta samu ƙuri'u mafi rinjaye a zaɓen 2023 da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng