Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Peter Obi Kan Zargin Tinubu Da Safarar Kwayoyi
- Kotun da ke sauraran kararrakin zaben shugaban kasa a Abuja ta yi fatali da karar Peter Obi
- Peter Obi da jam'iyyarsa ta Labour na kalubalantar zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa
- Har ila yau, su na zargin shugaban kasar da safarar miyagun kwayoyi a Amurka wanda hukumomi su ka kama shi a lokacin
FCT, Abuja - Kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta yi fatali da korafin jam'iyyar Labour kan safarar miyagun kwayoyi da ake kan Shugaba Tinubu.
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi na kalubalantar zaben da aka gudanar saboda tafka magudi, Legit.ng ta tattaro.
Meye kotun kan Peter Obi na zargin Tinubu?
Har ila yau, Peter Obi ya gaza kawo hujjoji kan cewa an taba kama Bola Tinubu a Amurka kan zargin safarar miyagun kwayoyi.
Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gamayyar lauyoyi biyar da Mai Shari'a Haruna Tsammani ke jagoranta shi ya yi fatali da karar, cewar Channels TV.
Ya ce babu wata hujja da dan takarar da jamiyyarsa su ka kawo da ta ke tabbatar da kama Tinubu kan zargin safarar kwayoyi a Amurka.
Ana zargin Bola Tinubu da safarar miyagun kwayoyi a Amurka wanda ya jawo masa asarar Dala dubu 460 kusan shekaru 30 baya.
Hukuncin kotun kan Peter Obi da Tinubu
A hukuncin yau, kotun ta ce babu wata tuhuma da aka yi wa Tinubu a kai don haka babu wata bukatar ci gaba da sauraran karar.
Kotun ta kara da cewa masu gabatar da kara ba su kawo kwararan hujjoji ba da za su tabbatar da kama kudaden a matsayin laifi.
Mai Shari'a Haruna Tsammani ya ce babu wata tara ko hukuncin zuwa gidan yari da zai tabbatar da hakan.
Tsammani ya ce a sashen kundin tsarin mulkin Najeriya na 137 ba ta hana Tinubu tsayawa takarar shugaban kasa ba.
Kotu Na Yanke Hukuncin Zaben Shugaban Kasa A Yau
A wani labarin, a yau Laraba 6 ga watan Satumba ne ake yanke hukunci kan shari'ar zaben shugaban kasa.
'Yan takarar jam'iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi na kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Faburairu kan magudin zabe.
Asali: Legit.ng