Kotu Ta Bayyana Natasha Akpoti a Matsayin Wacce Ta Lashe Zaben Sanatan Kogi ta Tsakiya
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna da ke zamanta a Lokoja, ta kwace kujerar sanatan APC
- Kotun ta sanar da Natasha Akpoti ta jam'iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaben sanatan Kogi ta Tsakiya
- Kotun ta bukaci sanatan na APC da ya biya Natasha kuɗaɗen da ta kashe wajen shigar da kara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Lokoja, jihar Kogi - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta bayyana Natasha Akpoti Uduaghan ta jam'iyyar PDP, a matsayin wacce ta lashe zaben sanatan Kogi ta Tsakiya a zaɓen 2023 da ya gabata.
Kotun ta yi wannan hukuncin ne a ranar Laraba, 6 ga watan Satumban shekarar 2023 kamar yadda AIT ta wallafa.
Natasha Akpoti ce ta lashe zaben sanatan Kogi ta Tsakiya
Shugaban kotun, mai shari'a K.A. Orjiakoin da ya yanke hukunci, ya ce Natasha ta jam’iyyar PDP, ta samu kuri’u 54,064, inda ta kayar da abokin hamayyarta Sadiku-Ohere na APC, wanda ya samu kuri’u 51,291.
Da Dumi-Dumi: Jam’iyyar Labour Ta Ki Amincewa Da Hukuncin Kotun Ƙararrakin Zabe, Ta Fadi Mataki Na Gaba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'ar ya bukaci Sadiku Ohere, da ya biya Natasha naira 500,000 kudin da ta kashe wajen shigar da kara.
An rage yawan ƙuri'un da Natasha ta samu a wasu akwatunan
A rahoton da jaridar Vanguard ta yi, an bayyana cewa an ƙarawa abokin takararta yawan ƙuri'u a wasu akwatuna guda tara a ƙaramar hukumar Ajaokuta ta jihar.
Hakanan an haɗa baki da wasu jami'an INEC, wajen rage yawan ƙuri'un Natasha a waɗancan akwatuna guda tara, tare da ƙin shigar da sakamakon wasu akwatuna uku da ta yi nasara.
Duk wannan kwamacalar sakamakon zaɓen dai ta faru ne a mazaɓar gwamnan jihar Kogi mai ci wato Gwamna Yahaya Bello.
Kotu ta tabbatar da nasarar sanatan APC a jihar Oyo
Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan nasarar sanatan Oyo ta Kudu, Sharafadeen Abiodun Alli na jam'iyyar APC, da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Oyo ta tabbatar.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da dan takarar sanata na jam'iyyar PDP, Joseph Tegbe ya shigar yana mai ƙalubalantar nasarar lashe zaɓen da Sanata Sharafadeen ya yi.
Asali: Legit.ng