Wani Jigon APC Ya Yi Garaje, Ya Fadi Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Zaben 2023

Wani Jigon APC Ya Yi Garaje, Ya Fadi Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Zaben 2023

  • Tolu Bankole bai jin tsoron Atiku Abubakar ko Peter Obi a shari’ar zaben shugaban kasa na 2023
  • ‘Dan siyasar kuma shugaba a jam’iyyar APC ya ce babu wanda ya isa ya yi wa Alkalai barazana
  • An taso kotun karar zabe a gaba domin a ruguza takarar Bola Tinubu ko a soke nasarar da ya samu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tolu Bankole ya na cikin shugabannin jam’iyyar APC na kasa, ya tofa albarkacin bakinsa kan hukuncin karar zaben shugaban kasa.

A ranar Talata, Punch ta rahoto Tolu Bankole ya na cewa alkalan da ke sauraron kotun korafin zaben 2023 za su ba APC gaskiya a hukuncinsu.

‘Dan siyasar ya bugi kirji ya na cewa ya na da tabbacin alkalan kotun daukaka karar za su tabbatar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe.

Kara karanta wannan

An Baza Jami’an Tsaro Kafin Tinubu, Atiku, Obi Za Su San Makomarsu a Kotu

Atiku, Tinubu, da Obi
Atiku, Tinubu, da Obi su na kotun zabe Hoto: @Atiku, @Dolusegun, @PeterObi
Asali: Twitter

An hurowa alkalan kotun zabe wuta

Hakan ya na zuwa ne sa’ilin da aka taso kotun da ke sauraron karar a gaba, ana jiran hukuncin da za a zartar watanni shida da ba APC mai-ci nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dauko alkalan da za su yi hukuncin ne daga kotunan daukaka kara na Asaba, Kano da Ibadan.

Shugaban masu rayuwa da nakasa a jam’iyyar APC na kasa ya hango wata galabarsu a kan Atiku Abubakar da Peter Obi duk da burin ‘yan adawa.

Bankole ya maida martani ne ga rahotannin da ke yawo cewa an hurowa kotun karar zaben shugaban kasa wuta ta rusa takarar da Tinubu ya yi.

Bukatar Atiku da Obi a kotun zaben 2023

Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar wanda ya yi takara a jam’iyyar PDP da Peter Obi na LP ne manyan abokan hamayyar Tinubu a zaben na bana.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP Ta Doke Abba Ganduje a Kotu a Karar Zaben ‘Dan Majalisa a Kano

Daga cikin bukatun wadanda su ka shigar da kara akwai maganar rashin cancantar shugaban kasa mai-ci ya tsaya takara a babban zabe tun da farko.

Lauyoyin PDP da LP sun zargi ‘dan takaran APC da rashin gabatar da gamsassun bayanai kan karatunsa da shari’ar da aka taba yi da shi a Amurka.

A wani jawabi da Bankole ya fitar a Abuja, ya nuna babu dalilin jin dar-dar, ya na mai ganin nasara ta na hannunsu, ya ce barazana ba za ta yi tasiri ba.

'Yan sanda sun cika Abuja

Duk wani wanda ya nemi tada tarzoma zai yabawa aya zaki, domin rahoto ya zo cewa dakarun ‘yan sanda sun fara sintiri a birnin tarayyan Abuja.

Za a haska zaman kotun a talabijin, ba a bukatar ganin kowa sai wanda aka tantance, an yi umarni ma’aikatan kotun daukaka kara su tsaya a gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng