Tinubu Ya Ce Ko Kadan Bai Damu Da Shari’a Kan Zaben Shugaban Kasa Ba Da Ake Shirin Yanke Hukunci
- Kotun sauraran kararrakin zabe da ke zamanta a Abuja ta sanar da ranar Laraba 6 ga watan Satumba don yanke hukunci
- Kotun ta sanar da haka ne don kawo karshen shari'ar da aka dade ana yi tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa da Shugaba Tinubu
- A ranar 1 ga watan Maris, Hukumar zabe ta sanar da Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe
FCT, Abuja – Yayin da ake dakon jiran hukuncin kotu na zaben shugaban kasa, Shugaba Bola Tinubu ya ce shi kam ko a jikinsa bai damu ba.
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Litinin 4 ga watan Satumba.
Meye Tinubu ke cewa kan shari'ar zabe?
Shari'ar Tinubu Da Obi: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Yadda Ubangiji Zai Turo Wakili Kan Shari'ar Zabe, Ya Bayyana Mai Nasara
Ajuri ya bayyana haka yayin da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels a Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ngelale ya ce ko kadan Shugaba Tinubu bai tsorata ba da sakamakon da kotun za ta sanar a ranar Laraba 6 ga watan Satumba.
Ya ce Tinubu bai damu ba ko kadan saboda yasan ya ci zabe kuma shi ne halastaccen shugaba wanda hukumar zabe ta sanar.
Ya ce:
“Ko kadan bai damu ba saboda yasan ya ci zaben da aka gudanar.”
Shugaba Tinubu zai tafi birnin New Delhi da ke Indiya a yau Litinin 4 ga watan Satumba da dare don halartar taron G-20, cewar Punch.
Har ila yau, za a sanar da sakamakon shari’ar da aka dade ana yi yayin da Tinubu ya ke kasar ketare.
Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan magatakardar kotun daukaka kara, Umar Bangai ya sanar da cewa kotun ta zabi ranar Laraba don yanke hukunci, cewar The Guardian.
A ranar 1 ga watan Maris, Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da Shugaba Bola Timubu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Faburairu.
Shari'ar Tinubu, Atiku, Obi: Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Ranar Laraba
A wani labarin, Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa za ta yanke hukunci kan shari'ar zaben da ke tsakanin Atiku Abubakar, Peter Obi da Shugaba Bola Tinubu.
Kotun zaben za ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba da muke ciki kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.
Asali: Legit.ng