Peter Obi Ya Lissafawa Kotu Bukatu 5 Da Yake So Ta Cika Ma Sa a Shari'arsa Da Tinubu

Peter Obi Ya Lissafawa Kotu Bukatu 5 Da Yake So Ta Cika Ma Sa a Shari'arsa Da Tinubu

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya shigar da ƙara a gaban kotun zaɓe, inda yake ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.

A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba ne dai ake sa ran kotun za ta yanke hukunci kan shari'ar ɗauki lokaci ana fafatawa.

Peter Obi dai ya shigar da ƙararsa ne tun cikin watan Maris ɗin shekarar 2023 kamar yadda Dakta Yunusa Tanko na jam'iyyar LP ya bayyana a shafinsa na X.

Obi ya miƙa buƙatunsa guda 5 gaban kotun zabe
Peter Obi bayyana buƙatunsa guda 5 da yake so kotu ta cika ma sa. Hoto: @OfficialABAT, @PeterObi
Asali: Twitter

Bukatu 5 da Peter Obi ya mikawa kotu a shari'arsa da Tinubu

A yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da dakon jin sakamakon shari'ar zaɓen a ranar Laraba mai zuwa, Legit.ng ta tattaro buƙatu biyar da Obi ya ke neman kotu ta cika ma sa.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku Da Obi: Jerin Kararraki 3 Da Aka Shigar Kan Tinubu a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

1. Soke cancatar Tinubu da Shettima

Daga cikin buƙatun da Peter Obi ya shigar a gaban kotu kamar yadda Premium Times ruwaito, akwai neman kotu ta soke cancatar Tinubu da Shettima na neman takara.

2. A ɓata nasarar Tinubu saboda rashin samun kaso 25% a Abuja

Buƙata ta biyu da Peter Obi ya shigar a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shi ne neman ɓata nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Obi ya dogara ne da cewa Tinubu bai samu kaso 25% na ƙuri'un da ake buƙata a babban birnin tarayya Abuja ba.

3. A soke zaɓen, a umarci INEC ta sake gudanar da zabe

Buƙata ta uku da Peter Obi ya mikawa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ita ce ta neman kotun ta soke zaɓen gaba ɗaya.

Haka nan ya buƙaci kotun ta tilasta Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), sake gudanar da sabon zaɓe.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Kotun Zaben Shugaban Kasa Za Ta Yi Hukunci Kan Makomar Tinubu, Atiku, Da Obi Cikin Satin Nan

4. A ayyana shi a matsayin shugaban ƙasa

Buƙata ta hudu da Peter Obi ya shigar ita ce ta neman kotun zaɓen ta ayyana shi a matsayin shugaban ƙasa saboda a cewarsa, shi ne ya lashe zaɓe.

Obi ya ce shi ne ya samu ƙuri'a mafi rinjaye a zaɓen da ya gudana a watan Fabrairun 2023, inda ya bukaci kotu ta ƙwatar ma sa haƙƙinsa, sannan ta tilastawa INEC ba shi satifiket.

5. Obi ya nemi kotu ta kashe zaɓen

Buƙata ta biyar ta ɗan takarar na jam'iyyar Labour ita ce ta neman kotu ta kashe zaɓen da ya bai wa Tinubu nasarar zama shugaban ƙasa.

Ya yi iƙirarin cewa ba a gudanar da zaɓen a bisa dokokin da aka tsara na gudanar da zaɓe ba.

Fasto ya fadi yadda Peter Obi zai karbe kujerar Tinubu

A wani labarin na daban da Legit.ng ta wallafa a baya, wani fasto mai suna Kingsley Okwukwe, ya bayyana cewa ɗan takarar jam'iyyar Labour wato Peter Obi, shi ne zai karɓe kujerar shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu Da Obi Za Su San Makomarsu Yayin Da Kotun Zaɓe Ta Sanar Da Lokacin Yanke Hukunci

Ya ce Ubangiji ya faɗa ma sa cewa zai turo wani mutum mai kama da Cyrus da zai ƙwace mulki daga hannun Tinubu ya mayar da shi hannun Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng