Atiku Vs Peter Obi: Kararraki 3 Da Aka Shigar Kan Tinubu a Gaban Kotun Zabe

Atiku Vs Peter Obi: Kararraki 3 Da Aka Shigar Kan Tinubu a Gaban Kotun Zabe

FCT, Abuja - Kotun daukaka ƙara ta bayyana ƙorafe-ƙorafe guda uku da ke gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, waɗanda ake tuhumar Bola Tinubu da su.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da kotun ta fitar shafinta na X.

Abubuwa 3 da ake karar Tinubu da su
Kararraki 3 da aka shigar a kan Tinubu a gaban kotun ƙararrakin zaɓe. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi
Asali: Twitter

Abubuwa 3 da ake ƙarar Tinubu da su a gaban kotu

Kamar yadda sanarwar ta shafin kotun ɗaukaka ƙarar ta bayyana, za a yanke hukunci ranar 6 ga watan Satumba da muke ciki. Korafe-korafen da kotun za ta duba su ne:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Korafin ɗan takarar jam'iyyar Labour (LP), Peter Obi, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da wasu mutane uku.

- Korafe-korafen jam'iyyar APM, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da wasu mutane huɗu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci

- Korafe-korafen ɗan takarar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da wasu mutane biyu.

Kotun ta kuma bayyana cewa a za a haska zaman kotun sauraron ƙararrakin zaɓen kai tsaye a gidajen talabijin ɗin ƙasar nan domin kowa ya shaida abinda ke wakana.

Kotun zabe ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan cewa an kusa zuwa ƙarshe kan ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, da abokinsa Peter Obi na jam'iyyar Labour.

Kotu ta tsayar da ranar Laraba, 6 ga watan Satumban nan da ake ciki domin yanke hukunci kan shari'ar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Atiku da Obi dai na ƙalubalantar nasarar lashe zaɓen da Tinubu ya yi a gaban kotu, inda suke fatan za ta soke zaben ko kuma ta ƙwace kujerar ta sa ta bai wa ɗaya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Kotun Zaben Shugaban Kasa Za Ta Yi Hukunci Kan Makomar Tinubu, Atiku, Da Obi Cikin Satin Nan

An bayyana yadda hukuncin kotun zaɓe zai kaya

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan hasashen da wani babban fasto, David Elijah ya yi kan shari'ar zaben shugaban ƙasa da ake yi tsakanin Atiku, Obi da kuma Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce ya hango a cikin wahayin da aka yi ma sa cewa ɗan takarar jam'iyyar Labour wato Peter Obi, zai hakura da shari'ar, matakin da ba zai yi wa masoyansa dadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng