Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu a Cikin Watan Satumba
- Sabon rahoto ya nuna cewa kotun zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke hukunci a cikin watan Satumba da ake ciki
- Lauyoyin Atiku, Tinubu da Peter Obi sun bayyana ra'ayoyinsu gabanin yanke hukuncin da kotun za ta yanke
- Sai dai an yi kira ga kotun da ta yanke hukunci bisa adalci ba tare da jin tsoron fadar shugaban ƙasa ba
FCT, Abuja - Kallo ya koma kan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, wacce za ta yanke hukunci dangane da shari'ar zaɓen da ke gudana a cikinta.
Jam'iyyar APC mai mulki tana fatan ganin hukunci kotun ya bai wa Bola Tinubu ikon ci gaba da zama a matsayin shugaban Najeriya.
Atiku da Obi na fatan ganin kotu ta ƙwace kujerar Tinubu
Dan takarar shugabancin ƙasa na PDP Atiku Abubakar, da Peter Obi na jam'iyyar Labour na fatan ganin kotun zaɓen ta yi abinda ba a taɓa yi ba a tarihin siyasar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suna ƙalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen da ya gabata, inda suke fatan kotun ta ƙwace kujerarsa ta miƙa ta ga ɗaya daga cikinsu.
An sha gumurzu da musayar yawu tsakanin lauyoyin da ke kare duka ɓangarorin a baya, inda daga ƙarshe kotu ta jingine yanke hukunci zuwa watan Satumba.
Sai dai mutane da dama sun yi kira da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen da kar wata barazana daga fadar shugaban ƙasa ta hana ta yin adalci.
Lauyoyin APC, PDP da LP sun yi tsokaci kan hukuncin kotun zaɓe
Yusuf Ali SAN, wanda mamba ne a cikin lauyoyin da ke kare Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana cewa yana da kyakkyawan zaton cewa hukuncin kotu zai yi wa wanda yake karewa daɗi.
Jaridar The Punch ta ruwaito daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar APC Bala Ibrahim na cewa hankalinsu a kwance yake saɓanin yadda jama'a ke yaɗawa.
Lauyan Atiku, kuma na jam'iyyar PDP, Mike Ozekhome SAN, ya yi kira ga kotun zaɓen da yi hukunci cikin adalci ba tare da jin tsoron kowa ba.
Lauyan Peter Obi da jam'iyyar Labour Kehinde Edun, ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan duk irin hukuncin da za ta yanke.
Primate Elijah ya hasaso juyin a ƙasashen Afrika 3
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan hasashen da shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya yi na cewa za a samun juyin mulki a ƙarin ƙasashen Afrika guda uku.
Ayodele ya ce akwai yiwuwar samun juyin mulki a ƙasashen ECOWAS biyu da kuma ƙasa ɗaya a Afrika ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng