Yadda Shaidan PDP Ya Tabbatarwa Kotu Ni Na Ci Zaben Bana, Gwamna Uba Sani Ya Magantu
- Gwamnan jihar Kaduna na yanzu ya bayyana kwarin gwiwar yin nasara a kotun sauraran kararrakin zabe da ke zama a yanzu
- Ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, bai da bukatar ba da wasu Karin shaidu, domin PDP ta yi aikin rusa kanta a kotun zaben
- Jam’iyyar PDP ta kalubalanci yadda aka ba Uba Sani nasara a zaben gwamnan da aka gudanar a farkon shekarar nan
Jihar Kaduna - Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna, ya yi ikirarin cewa jam’iyyar PDP, yayin da take kalubalantar nasararsa, ta taimaka wajen tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, rahoton Vanguard.
Ya fadi hakan ne jawabinsa na karshe ga kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna, gwamnan ta hannun tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Cif Bayo Ojo, tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a.
Jam’iyyar PDP da dan takararta Mohammed Ashiru Isa na kalubalantar ayyana Sani na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar.
Martanin Uba Sani
Gwamna Sani ya ci gaba da cewa, wadanda suka shigar da kara, PDP da Isa sun tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaben duba da abin da suka gabatar a kotun, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bakin lauyoyinsa, gwamnan ya ce bai ga dalilin da zai sa ya kira shaida ba, domin ya tattara isassun shaidu a lokacin sauraron kararrakin don lallasa jam’iyyar PDP da Isa kan rashin kawo hujjojin da suka dace a gaban kotun.
Sani yace:
“A karkashin binciken kotu, wannan shaida ya yarda cewa bai halarci komai na zaben ba ta kowace fuska a ranar zaben. Mafi mahimmanci, PW1 (Gwazah) ya yarda da hakan.”
APC ta tsure da hujjojin APC
A wani rahoton Legit.ng na baya, gwamna Uba Sani bai yarda da hujjojin da ake kokarin ayi amfani da su daga hukumar INEC a gaban kotun sauraron karar zaben shi ba.
Baya ga kin amincewa ayi amfani da wadannan takardu, Daily Trust ta ce Mai girma Uba Sani ya na so kotu tayi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta kai.
Lauyan da yake kare Uba Sani wanda shi ne ‘dan takaran APC a zaben bana, ya soki karar PDP.
Asali: Legit.ng