Tuggar, Edun da Jerin Ministoci 4 da Za Su Yi wa Tinubu Rakiya Zuwa Taron G20 a Indiya

Tuggar, Edun da Jerin Ministoci 4 da Za Su Yi wa Tinubu Rakiya Zuwa Taron G20 a Indiya

  • Shugaban kasar Najeriya zai tafi babban birnin Indiya domin halartar taron kungiyoyin kasashen G-20
  • Akwai daidaikun ministocin da aka ware domin su tafi birnin New Delhi tare da Mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • A tawagar Tinubu akwai ministan tattalin arziki da ministocin sadarwa da kirkire-kirkire da na masana’antu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya zuwa kasar Indiya domin ya halarci taron kungiyoyin G-20 da za ayi a birnin New Delhi.

Firayin Ministan Narendra Modi ya aikawa takwaransa watau Bola Ahmed Tinubu gayyata ta musamman kamar yadda aka sanar.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya ce gobe za a shilla zuwa Delhi. Daily Trust ta tabbatar da rahoton nan dazu.

Tinubu
Shugaban Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tawagar Mai girma Shugaba Bola Tinubu ta na dauke da wasu daga cikin ministocinsa wanda su ka shiga ofis a watan Agusta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tinubu zai shilla kasar waje domin halartar wani muhimmin taro

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ministocin da za su raka Tinubu zuwa Indiya

1. Amb. Yusuf Tuggar

2. Adebayo Wale Edun

3. Dr. Bosun Tijani

4. Dr. Doris Uzoka-Anite

Amb. Yusuf Tuggar shi ne sabon ministan harkokin wajen Najeriya, kafin rike wannan mukami, shi ne jakadan Najeriya a kasar Jamus.

Shi kuma Adebayo Wale Edun zai halarci taron a matsayin babban ministan da aka ratayawa akalar tattalin arzikin Najeriya da harkar kudi.

Ministan tattalin arzikin zamani, sadarwa da kirkire-kirkire, Dr. Bosun Tijani ya na cikin ‘yan tawagar da za a gani wajen taron kungiyar G20.

Rahoton ya ce Dr. Doris Uzoka-Anite wanda mace da ke jagorantar ma’aikatar kasuwanci, masana’antu da hannun jari za ta yi rakiyar.

Ngelale ya ce gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da taron domin jawo hannun jari daga ketare.

Ana sa ran a dalilin taron da za ayi a kasar Indiyar, matasan Najeriya su samu ayyukan yi, sannan hakan ya bunkasa karfin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Farashin Litar Man Fetur Zata Faɗi Warwas Ta Dawo Ƙasa da N200 a Najeriya Idan Aka Yi Abu 1

Tinubu ya ba matashi rikon NASENI

Ku na da labari wani matashi daga Kano ne Bola Ahmed Tinubu ya nada ya jagoranci hukumar NASENI ta kasa bayan ya tsige Dr. Bashir Gwandu.

Lokacin da gwamnatin tarayya ta kirkiro NASENI, watakila Khalil Suleiman Halilu bai wuce shekara daya ba, yanzu haka shekaransa 32 ne rak.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng