Watanni 3 da Sauka Da Barin Mulki, Babbar Hadimar Buhari na Neman Rasa Gidan Zama

Watanni 3 da Sauka Da Barin Mulki, Babbar Hadimar Buhari na Neman Rasa Gidan Zama

  • An zargi Lauretta Onochie da kutsawa gidan wasu Bayin Allah a Ingila, ta na kokarin ta ci zarafinsu
  • Daga baya jagorarta APC ta ce ba haka abin yake ba, gidanta ne ta dauko ta ba wani ‘danuwanta aro
  • Onochie take cewa iyalin Victor Ashiedu Fejokwu ba su da niyyar barin gidan, sai ta kira masu ‘yan sanda

United Kingdom - Lauretta Onochie wanda ta yi aiki da Muhammadu Buhari ta samu kan ta a cikin matsalar matsuguni a kasar Birtaniya.

Watanni uku da sauka daga kujerar da ta ke kai na shugaban majalisar da ke kula da aikin NDDC, asirin ‘yar siyasar na neman ya tonu a Ingila.

A ranar Alhamis, rahoto ya zo cewa Bola Tinubu ya tsige majalisar da Onochie ta ke jagoranta, ya nadawa NDDC wasu sababbin shugabanni.

Kara karanta wannan

“Za a Iya Korarka Daga PDP” ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Kaca-Kaca da Wike

Lauretta Onochie
Lauretta Onochie da Muhammadu Buhari Hoto: @Laurestar
Asali: Twitter

Bidiyon Lauretta Onochie

Wani bidiyo ya bulla a dandalin sada zumunta inda aka ga Onochie ta na rigima da wasu ‘yanuwanta a kan wani gida ta ce ita ta mallaka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Edafe Larry da yake bayani a Twitter, ya zargi tsohuwar hadimar shugaban Najeriya da neman korar wasu mutane daga gidansu a birnin Landan.

A cewarsa, Onochie wanda ta yi aiki da Shugaba Muhammadu Buhari ta auka masu ba tare da sanarwa ba, ta nemi ta kore su daga cikin gidansu.

Kamar yadda Sahara Reporters ta dauko bidiyon, wani karamin yaro ya rika korar tsohuwar shugabar majalisar da ke kula da NDDC daga dakinsa.

Har wannan karamin yaro ya na cewa zai kira mata ‘yan sanda domin bai san ta ba, ya na kuma zarginta da ci masa zarafi tun da ta auko masu gida.

Kara karanta wannan

'Wike Zai Kare a Gidan Yari', Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Shiga Kotu

An yi rana, sun yi dare

A yayin da ta tashi karin bayani a Twitter, Onochie ta ce abin da ya faru shi ne, ita ce ta taimakawa ‘danuwanta mai suna Victor Ashiedu Fejokwu wurin zama.

Daga baya sai Victor Ashiedu Fejokwu da mai dakinsa, Ruth Emereze, su ka juya mata baya alhali ta cece su a lokacin da su ka yi carko carko a Landan.

Zuwa yanzu da ta zo karbar gidanta sai abin ya gagara domin sun canza mabudi, abin ne ya jawo ta hada da ‘yan sandan kasar Birtaniya domin a fatattake ta.

Tinubu zai yaki Nijar

Idan yaki ya barke da Nijar, ku na da labari tsohon jigo a APC mai mulki, Dr. Usman Bugaje ya ce za a iya samun tasgaro a shari’ar zaben shugaban kasa.

Tsohon ‘dan majalisar ya na ganin akwai kullaliya tsakanin Nijar da NADECO wanda Bola Tinubu mai neman sabun karbuwa a Turai ya taba zama 'dan ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng