Ni ba yar jam’iyyar APC bace, Hadimar Buhari Lauretta Onochie ta bayyanawa Majalisa
- Misis Laurette Onochie ya bayyana gaban majalisar dokoki
- Ta musanta kasancewa zama yar jam'iyyar APC
- Jam'iyyar PDP tace ba zata yarda a nada Lauretta
Hadimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan kafafen yada labaran zamani, Misis Lauretta Onochie, ta bayyanawa kwamitin majalisar dattawa cewa ita ba ’yar jam’iyyar APC ko PDP bace.
Onochie wacce ta kasance yar gani kashenin Shugaba Buhari ta fadawa majalisar cewa ba tada jam’iyyar siyasa.
Ta bayyana hakan ne yayinda ta bayyana gaban majalisar ranar Alhamis domin tantanceta matsayin sabuwar kwamishana a hukumar gudanar da zabe ta kasa watau, INEC.
Kamar dai yadda dan jaridar Arise News Sumner Sambo ya ruwaito,
Tace:
“Ni ba mambar wata jam’iyyar siyasa bace”.
Lauretta Onochie ta kasance cikin yan a mutu Buhari da jam’iyyar APC.
Wannan maganar ya baiwa mutane mamaki saboda sai tayi rantsuwa da littafi mai tsarki cewa duk abinda zata fadawa yan majalisar gaskiya ne.
DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota
PDP tayi zanga-zanga
Daily Trust ta fitar da rahoto cewa a yau ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, 2021, wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, sun shirya zanga-zanga a majalisar tarayya.
‘Yan jam’iyyar adawar sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne domin nuna rashin amincewarsu a kan shirin ba Misis Lauretta Onochie mukami.
Onochie ta na cikin masu taimaka wa shugaban Najeriya wajen harkar yada labarai ta kafafen zamani.
Asali: Legit.ng