"LP Ko APC": Shehu Sani Ya Bayyana Jam'iyyar Da Za Ta Ci Ribar Rikicin Siyasar Jihar Edo
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana matsayarsa kan rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Edo
- Sani wanda ya bayyana takun saƙar da ke tsakanin gwamna Obaseki da Philip Shaibu a matsayin yaƙi, ya ce LP ko APC za su ci gajiyar rigimar
- Hakan na zuwa ne bayan gwamnan ya fitar da mataimakin gwamnan daga gidan gwamnati inda ya mayar masa da ofishinsa a wajen gidan gwamnati
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana matsayarsa kan takun saƙar da ke faruwa a tsakanin gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da mataimakinsa, Philip Shaibu.
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka sani da Twitter) a ranar Asabar, 2 ga watan Satumba, tsohon sanatan ya bayyana waɗanda za su ci ribar faɗan da ake yi.
Tsohon sanatan na majalisar dattawa ta takwas wanda ya bayyana takun saƙar a matsayin yaƙi, ya ce jam'iyyar Labour Party (LP) ko jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za su amfana daga wannan rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Edo.
Shehu Sani ya rubuta cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Edo; yaƙin Obaseki da Shuaibu zai amfani jam'iyyar LP or APC."
Ƴan Najeriya sun yi martani kan kalaman Shehu Sani
Ƴan Najeriya kamar yadda aka saba sun garzaya sashen bayani inda suka yi martani kan kalaman Shehu Sani.
@raylex04 ya rubuta:
"Zai amfane ni da iyalai na."
@JaypeeGeneraI ya rubuta:
"Jam'iyyar Elluu Pee ce za ta yi nasara."
@AbdullAhmad30 ya rubuta: "
"Wataƙila LP ta amfana daga rikicin."
@Onyeckerous ya rubuta:
"LP ta riga da ta yi nasara."
@CallMeHabeeb ya rubuta:
"Obaseki ya riga da ya san cewa lokacinsa ya ƙare a jihar Edo. Ko zaɓen kansila ba zai iya ci ba yanzu."
Obaseki Ya Sauyawa Obaseki Ofis
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sauyawa mataimakinsa, Philip Shaibu, ofis daga gidan gwamnatin jihar saboda takun saƙsr da su ke yi.
Gwamnan ya fitar da ofishin mataimakin gwamnan ne daga gidan gwamnatin ne bayan rikicin siyasar da ke faruwa a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng