Tinubu Zai Halarci Taron G20 Da Zai Gudana a New Delhi Na Kasar Indiya
- Shugaba Bola Tinubu zai shilla zuwa Indiya domin taron halartar taron ƙasashen G20
- Taron zai gudana ne a ranar tara da kuma 10 ga watan Satumban nan da muke ciki
- Za a tattauna muhimman abubuwa da za su kawowa Najeriya ci gaba a yayin gudanar da taron
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai tafi zuwa birnin New Delhi na ƙasar Indiya domin halartar taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na G20.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Cif Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati.
Me zai kai Tinubu wajen taron na G20 na bana?
Taron G20 na bana dai zai gudana ne a New Delhi, babban birnin ƙasar Indiya a ranakun tara da 10 ga watan Satumban nan da muke ciki kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ajuri ya bayyana cewa a yayin taron, Shugaba Bola Tinubu zai haɗu da takwarorinsa shugabannin ƙasashe daga sassa daban-daban na duniya.
Ya ƙara da cewa Tinubu zai gabatar da jawabi a gaban shugabannin duniya da kuma manyan 'yan kasuwa masu zuba hannayen jari.
Amfanin taron na G20 ga Najeriya
Ajuri Ngelale ya ƙara da cewa a yayin taron Shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na Brazil, Firaministan Indiya, shugaban ƙasar Koriya ta Kudu da shugaban gwamnatin Jamus.
Ya kuma ce Tinubu zai gana da shugabannin manyan kamfanoni na duniya, inda ake sa ran zai janyo wasu daga cikinsu domin su zo su zuba hannayen jari a Najeriya.
Ngelale ya kuma tabbatar da cewa shugaban zai yi amfani da wannan dama ta halartar taron wajen ganin an kawowa Najeriya wani abu na ci gaban 'yan ƙasa kamar yadda New Telegraph ta wallafa.
Ƙasashen na G20 dai su ne; Argentina, Australia, Brazil, Canada, China, Faransa, Jamus, Indiya, Indonesia, Italiya, Japan, Koriya ta Kudu, Mexico, Rasha, Saudi Arabia, Afrika ta Kudu, Turkiya, Ingila, da Amurka, sai kuma tarayyar Turai (EU).
Wike ya ce Tinubu yake yi wa aiki ba APC ba
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan iƙirarin da ministan birnin tarayya Nyesom Wike ya yi na cewa Shugaba Tinubu yake yi wa aiki ba jam'iyyar APC mai mulki ba.
Wike ya kuma jaddada cewa har yanzu yana nan a cikin jam'iyyarsa ta PDP babu wanda ya isa ya dakatar da shi.
Asali: Legit.ng