Wata qasa ta gargadi Yariman Saudiyya da kada ya kuskura ya tako yazo musu ziyara

Wata qasa ta gargadi Yariman Saudiyya da kada ya kuskura ya tako yazo musu ziyara

- Shuwagabannin Argentina sun gargadi Yariman Saudiyya

- Kada ya kuskura ya taka kasar su don halartar taron G20

- Idan ya sake ya tako kuwa, zai yi nadama

Wata qasa ta gargadi Yariman Saudiyya da kada ya kuskura ya tako yazo musu ziyara
Wata qasa ta gargadi Yariman Saudiyya da kada ya kuskura ya tako yazo musu ziyara
Asali: Getty Images

Shuwagabannin kasar Argentina su gargadi Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman da kada ya kuskura ya tako kasar su don halartar taron G20 da kasar zata karbi bakunci a watan Nuwamba.

Kasar Argentina ta zurafafa bincike akan rawar da shugabannin Saudiyya musamman Muhammad Bin Salman akan rikicin Yaman da kisan gillar da akayi wa Dan jarida Kashoggi.

A yayin da suke magana da manema labarai, shuwagabanni kasar Argentina sun ce: " Matukar ya tako kasar mu da nufin taron G20, to zamu gurfanar dashi a gaban kuliya."

DUBA WANNAN: An sako 'yar takarar shugaban kasa a gaba kan shugaba Buhari

Shugaban hukumar kare hakkin bil adama na kasar ta Argentina, Kenneth Roth cewa yayi, " Yakamata shuwagabanni su nuna wa Bin Salman cewa babu wanda yafi karfin shari'a. Idan ya sake ya tako kasar Argentina to babu makawa zai yi daya sani,domin zamu kaishi gaban kuliya."

An dai sake gano wa ashe cikin mintuna bakwai kacal da shigar Khasshoggi ofishin Turkiyyar aka hallaka shi, ba wai ya wani dade ne a ciki ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel