Shettima Ya Bukaci Masu Son Yi Ma Sa Murnar Ranar Haihuwa Da Kar Su Wallafa Sakonsu a Jaridu

Shettima Ya Bukaci Masu Son Yi Ma Sa Murnar Ranar Haihuwa Da Kar Su Wallafa Sakonsu a Jaridu

  • Kashim Shettima ya nemi masoyansa da su canja tsarin da suke bi wajen taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa
  • Ya miƙa godiyarsa a garesu inda ya buƙaci su taimaki mutane da kuɗaɗen da za su kashe wajen wallafa saƙonninsu a jaridu
  • Kashim ya yi la'akari da halin ƙuncin da ake ciki ne wajen faɗawa masoyan na sa abinda yake so

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nemi masoyansa su canja yadda suke taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa daga yadda suke yi a baya.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kashim Shettima ya miƙa godiyarsa ga masoyansa kan abubuwan da suka ma sa a baya.

Shettima ya buƙaci masoyansa da kar su wallafa saƙon taya shi murna a jaridu
Shettima ya bukaci masoyansa su taimaki mabuƙata da kuɗaɗen da za su kashe wajen taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Shettima ya bukaci masoyansa da kar su wallafa sakonsu a jaridu

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Fadi Ainihin Abinda Ya Janyo Matsalar Tsaro a Yankin Arewa Maso Yamma

Sai dai a wannan karon, Shettima ya buƙaci masoyan na sa da masu fatan alkahiri da su guji wallafa saƙon murnar a jaridu ko wasu kafafe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bisa la'akari da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa, yana kira ga masoyan na sa da su yi amfani da kuɗaɗen wajen tallafawa mabuƙata.

a ranar Asabar mai zuwa, wato 2 ga watan Satumba da muke ciki ne Kashim Shettima ke cika shekaru 57 a duniya.

Rashin shugabanci nagari ne ya janyo matsalar tsaro

A baya Legit.ng ta yi wani rahoto inda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa rashin samun ingantaccen shugabanci ne ya janyo matsalar tsaro a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shettima ya ce akwai buƙatar masu ruwa da tsaki na yanki su haɗu domin kawo tsare-tsaren da za su ciyar da yankin gaba, wanda hakan zai taimaka wajen magance matsalolin tsaron.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Ba Da Umarnin Rufe Makaranta Saboda Mummunan Laifin Da Aka Aikata a Cikinta

Ya bayyana hakan ne a yayin da wata kungiya ta gamayyar 'yan kasuwa daga Arewa maso Yamma suka kai ma sa ziyara a fadar gwamnati.

Tinubu ya ware biliyan 50 don sake gina Arewacin Najeriya

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan maƙudan kuɗaɗen shugaban ƙasa ya ware domin sake gina yankin Arewacin Najeriya da matsalar tsaro ta yi wa lahani.

Da yake ba da bayani, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya bayyana cewa naira biliyan 50 shugaban ya ware domin gyara yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng