“PDP Za Ta Kori Nyesom Wike”: Hadimin Atiku Ya Fadi Mataki Na Gaba Da Jam’iyyar Za Ta Dauka
- Wani jigon jam'iyyar PDP ya bayyana abun da shugabancin jam'iyyar za su yi wa tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan Abuja, Nyesom Wike
- Hadinin dan takarar shugaban kasa na PDP, Daniel Bwala, ya bayyana cewa ba dakatar da Wike kawai jam'iyyar za ta yi ba, har ma da korarsa
- A cewar Bwala, an san Wike da dirama amma shirun PDP ba rauni bane kuma za a yi abun da ya dace a lokacin da ya dace
Daniel Bwala, tsohon kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku Abubakar a zaben 2023 ya bayyana irin hukuncin da za a yankewa Nyesom Wike, ministan Abuja.
PDP za ta fatattaki Wike daga jam'iyyar a lokacin da ya dace, Bwala
A cewarsa, za a kori Wike daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a lokacin da ya dace.
Bwala ya yi magana ne a wata hira da Channels TV a shirin Politics Today a daren ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Wike ya kalubalanci PDP da ta dakatar da shi don ya goyi bayan zaben shugaban kasa Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma aiki a majalisarsa a matsayin minista.
"Abun da yasa bamu cika mayar da martani ga abun da shi (Wike) yake fadi ba shi ne saboda yana son dirama, kowa ya san wannan," inji Bwala.
"Shirun jama'iyyar ba rauni bane...jam'iyyar ta san abun da take yi. A lokacin da ya kamata, ba dakatar da shi (Wike) za a yi kawai ba har ma da korarsa. Ku rubuta ku ajiye," Cewar Bwala.
Jigon na PDP ya ce koda dai Wike na da karfin inganta babban birnin tarayya, shi 'kwamishina mai daukaka ne” wanda bai kamata ya rika daukar ikon gwamnan jiha a kan karan kansa ba."
Wike ya bayyana yadda gwamnonin PDP suka dunga zawarcin mukamai a gwamnatin Tinubu
A wani labarin, mun ji cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya kira wadanda ke kira ga dakatar da shi daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin "yan rawan nanaye".
Wike, wanda ya rike mukamin gwamnan jihar Ribas sau biyu a karkashin jam'iyyar PDP ya yi martanin ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin minista a karkashin gwamnatin jam'iyyar APC a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng