Shugaba Tinubu Ya Ce Sojojin Gabon Sun Tabbatar Ma Sa Da Abinda Yake Fargaba Game Da Nijar
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa abinda yake tsoro ne ya faru a ƙasar Gabon
- Ya ce ya hasaso cewa sojojin wasu ƙasashen za su yi ƙoƙarin kwaikwayon abinda sojin Nijar suka yi
- Ya bayyana hakan ne a yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III a Abuja
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa abinda yake gujewa bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar, ya tabbata a juyin mulkin da sojoji suka yi wa Ali Bongo na Gabon.
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, a lokacin da ya karbi baƙuncin Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar III.
Sojojin Gabon sun tabbatar da abinda Tinubu yake fargaba
Tinubu ya bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kawo ƙarshen rikicin Nijar ta hanyoyi na diflomasiyya, kafin a kai ga zuwa yaƙi, wato mataki na ƙarshe da za a iya ɗauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya jaddada cewa duk wani nau'i na ƙwatar mulki da sojoji suke yi daga hannun farar hula, abin a yi Allah wadai ne da shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu ya ƙara da cewa juyin mulkin da aka gudanar a ƙasar Gabon ya tabbatar da abinda yake tsoro na cewar sojojin wasu ƙasashen za su kwaikwayi abinda aka yi a Nijar.
Da safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Agusta ne aka wayi gari da juyin mulkin da sojoji suka yi wa Ali Bongo na ƙasar Gabon.
Tinubu ya ce Najeriya ba ta son yakar Nijar
Shugaba Tinubu Ya Maida Martani Kan Sabon Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Gabon, Ya Faɗi Mataki Na Gaba
Tinubu ya godewa Sarkin Musulmi bisa ziyarce-ziyarcen da suka kai jamhuriyar Nijar, inda ya shaida ma sa cewa za su ƙara komawa domin a kawo ƙarshen rikicin.
Ya ce Najeriya ba za ta yaƙi jamhuriyar Nijar ba kasantuwarta maƙwabciyarta, wacce kuma take da alaƙa ta ɓangarori da dama da ita kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Ya ƙara da cewa kowa na ganin abinda yaƙi ya janyo a Ukraine da kuma Sudan, sai dai ya ce hakan ba yana nufin za a zura ido a bar abinda ya faru a Nijar ɗin ya ci gaba da faruwa ba.
Tinubu ya kuma bayyana cewa suna sane da halin da 'yan Nijar suke ciki, a dalilin hakan ne suke son sojojin su yi abinda ya kamata domin a cirewa ƙasar takunkuman da aka sanya ma ta.
Tinubu ya yi martani kan juyin mulkin Gabon
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Gabon da Tinubu ya yi.
Tinubu ya ce ba za su lamunci abinda ke faruwa a ƙasashen Afrika ba, kuma za su yi aiki tare da kungiyar Tarayyar Afrika don ganin an ɗauki mataki a kan Gabon.
Asali: Legit.ng