Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: 'Yan Najeriya Sun Bukaci Kotun Zabe Ta Yi Gaskiya Da Adalci Yayin Yanke Hukunci

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: 'Yan Najeriya Sun Bukaci Kotun Zabe Ta Yi Gaskiya Da Adalci Yayin Yanke Hukunci

  • An bukaci kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa da ta yi adalci wajen yanke hukunci
  • Wata kungiya ta 'yan Najeriya mai suna CCN ce ta miƙa wannan buƙata ga shugaban kotun zaɓen mai shari'a Haruna Tsammani
  • Ƙungiyar tare da ƙarin wasu 'yan Najeriya sun miƙa buƙatar ta su a rubuce ta neman a yi hukuncin cikin gaskiya da adalci

Wata kungiya ta 'yan Najeriya “Coalition of Concerned Nigerians (CCN)” tare da wasu 'yan Najeriya sama da 100, sun miƙa buƙatarsu ga kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa (PEPC).

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, hakan na ƙunshe ne a cikin wani koke da suka aika a rubuce ga shugaban kotun mai shari'a Haruna Tsammani.

An bukaci kotun zaɓe ta yi adalci a shari'ar Atiku, Obi da Tinubu
An bukaci kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi adalci a shari'ar Atiku, Obi da Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi
Asali: Twitter

An bukaci kotun ta yi hukunci cikin gaskiya da adalci

Ƙungiyar ta buƙaci kotun da ta gabatar da shari'ar cikin gaskiya da adalci, wacce za ta yi wa 'yan Najeriya daɗi ba tare da nuna wani son rai ba.

Kara karanta wannan

Kansiloli Sun Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Da Ya Zargi Gwamna Da Karkatar Da Kudade

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin koken, ƙungiyar ta bayyana cewa 'yan Najeriya da ke gida da waje sun dogara ne da hukuncin da kotun za ta yanke kan zaɓen wajen samun kwarin gwiwa kan al'amuran ƙasar.

Koken ya kuma bayyana cewa wannan wata dama ce ga duka alƙalan kotun domin a riƙa tunawa da su a matsayin waɗanda suka yanke hukunci na adalci.

Fasto ya yi hasashen yadda shari'ar zaɓen shugaban ƙasa za ta ƙare

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan hasashen da babban fasto David Elijah ya yi kan yadda ƙarshen shari'ar zaɓen shugaban ƙasa za ta kaya.

Faston ya bayyana cewa ɗan takarar jam'iyyar Labour wato Peter Obi, zai haƙura da ƙarar da ya shigar saboda samun zaman lafiya, matakin da cewarsa zai sa mutanensa su ji haushinsa.

Kara karanta wannan

Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Shugaban Jam'iyya Ya Faɗi Wanda Yake da Tabbacin Zai Samu Nasara a Kotu

Ya shawarci magoya bayan Peter Obi kan cewa su sanya a ransu cewa ɗan takarar na su zai haƙura da ƙarar da ya shigar.

Shugaban Labour ya ce Peter Obi zai amshe kujerar Tinubu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan iƙirarin da shugaban jam'iyyar Labour na ƙasa, Julius Abure ya yi na cewa nan ba da jimawa ba kotu za ta ayyana Peter Obi a matsayin sabon shugaban Najeriya.

Abure ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan Najeriya mazauna ƙasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng