Dalilin Da Yasa Na Yi Mamaki Da Tinubu Ya Nada Ni Ministan Abuja, Wike
- Nyesom Wike ya bayyana cewa nadinsa a matsayin ministan babban birnin tarayya ba abu ne da ya yi tsammani ba
- Wike ya kasance babban jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon gwamnan jihar Ribas
- Dan siyasar mai shekaru 55 ya yi godiya ga Shugaban kasa Bola Tinubu kan ganin cancantarsa da ya yi a matsayin ministan Abuja
FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa nadinsa ba abu ne da ya sa rai ba.
Da yake jawabi a wata hira da Channels TV a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa ya yi mamaki lokacin da ya samu labarin nadin nasa a matsayin ministan Abuja.
"Mukamin minista ba abu ne da na shirya ba", Wike
Ya nuna godiyarsa ga Shugaban kasa Bola Tinubu kan karrama shi da ya yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kwanaki ne Shugaban kasa Tinubu wanda ya lashe zabe a inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya nada Wike a matsayin ministan Abuja domin ya yi aiki a majalisarsa.
Nadin Wike a matsayin minista ya janyo cece-kuce kasancewarsa babban jigo na babbar jam'iyyar adawa, ta Peoples Democratic Party (PDP).
A halin da ake ciki, an yarda cewa Wike ya yi aiki don nasarar Tinubu a zaben watan Fabrairun 2023.
Wike ya ce:
"Ban taba hango kaina a matsayin ministan Abuja ba daidai da rana daya. Wannan ne dalilin da yasa na yi mamaki lokacin da aka sanar cewa shugaban kasar ya ga cewa nine na dace na zama ministan Abuja. Ba abu ne da na shirya ba, ba abu ne da na yi tunanin zai iya faruwa ba. Amma sai ga mu a nan. Saboda haka, nagode mai girma shugaban kasa, kuma nagode wa Allah madaukakin sarki."
Ya ci gaba da cewa:
"Ina ganin dole shugaban kasar ya hango tarin nasarata a matsayin gwamna."
Wike ya sake takalo Atiku da PDP da fada
A wani labarin, mun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake yin shaguɓe ga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar nan, Peoples Democratic Party (PDP).
Tsohon gwamnan na jihar Rivers wanda aka tattauna da shi a gidan talbijin na Channels tv a shirinsu na Politics Today a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, ya ƙalubalanci shugabannin jam'iyyar PDP, idan sun isa su dakatar ko ladabtar da shi.
Asali: Legit.ng