Nyesom Wike Ya Sake Takalar Fada Tsakaninsa Da Atiku, PDP
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa bai ci dunduniyar jam'iyyarsa ba
- Wike ya yi nuni da cewa ya rubutawa PDP wasiƙa dangane da kujerar ministan da aka ba shi amma bai samu amsa daga shugabannin jam'iyyar ba
- Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya haƙiƙance cewa shugabannin jam'iyyar ba za su iya dakatar da shi ba saboda su ne suka saɓa kan kundin tsarin mulkin PDP
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake yin shaguɓe ga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar nan, Peoples Democratic Party (PDP).
Tsohon gwamnan na jihar Rivers wanda aka tattauna da shi a gidan talbijin na Channels tv a shirinsu na Politics Today a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, ya ƙalubalanci shugabannin jam'iyyar PDP, idan sun isa su dakatar ko ladabtar da shi.
Babu wanda ya isa ya dakatar da ni, Wike
Wike ya bayyana cewa bai ga wani jigo a jam'iyyar ba wanda zai iya dakatar da shi ko korarsa daga jam'iyyar ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Waye zai ladabtar da ni? Ni ne yakamata na riƙa kira kan a ladabtar da waɗanda suka yi wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar karan tsaye, inda jam'iyyar ta goyi bayan karɓa-karɓa"
"Waye zai dakatar da ni? Ina son na ga wanda ya isa."
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sai da ya sanar da shugabancin jam'iyyar PDP kafin ya karɓi tayin kujerar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar Progressives Congress (APC), ya yi masa.
"Da Obi ya cancanta da ya samu ƙuri'un ƴan Najeriya": Cewar Wike
Nyesom Wike ya yi magana kan nasarar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya samu a zaɓe, da ƙaddarar da ta auka akan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.
Wike ya bayyana cewa da a ce Peter Obi shi ne ɗan takarar da ya fi cancanta, tabbas da ƴan Najeriya sun zaɓe shi a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Wike Shugaba Tinubu Ya Ke Yi Wa Aiki
Rahoto ya zo cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana wanda ya ke yi wa aiki a tsakanin jam'iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu.
Miinistan na birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ke yi wa aiki ba jam'iyyar APC, kuma yana nan daram a jam'iyyarsa ta PDP.
Asali: Legit.ng