Shugaba Tinubu Na Ke Yi Wa Aiki Ba Jam'iyyar APC Ba, Nyesom Wike
- Toshon gwamnan jihar Ribas kuma ministan Abuja ya ce Tinubu yake wa aiki ba jam'iyyar APC ba
- Nyesom Wike ya jaddada cewa yana nan daram a jam'iyyar PDP kuma ba bu wanda ya isa ya dakatar da shi
- An ƙara shiga ruɗanin kan siyasar Wike bayan sunansa ya shiga kwamitin kamfen APC na zaben Baylesa
FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya fayyace gaskiya cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yake yi wa aiki ba jam'iyyar APC ba.
Mista Wike ya bayyana haka ne yayin da ya bakunci shirin Siyasa a Yau na gidan talabijin na Channels ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, 2023.
Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma Ministan Abuja, Wike ya ce:
“Ba jam'iyyar APC nake yi wa aiki ba. Shugaba Tinubu nake wa aiki, wanda ya aminta da ni domin na taimaka masa ya cika burinsa na sabunta fatan 'yan Najeriya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba bu wanda ke bina bashin neman yafiya ko wanda zan ba haƙuri. Ina cikin jam'iyyar PDP kuma na yi wa Ahmed Bola Tinubu aiki ya zama shugaban Najeriya.”
Jaridar Punch ta rahoto cewa an sake shiga ruɗani bayan ganin sunan Wike a cikin kwamitin yaƙin neman zaben APC na zaɓen gwamnan da ke tafe a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa.
Sai dai da daren ranar Talata, jam'iyyar APC ta musanta sakin jerin sunayen mambobin kwamitin kamfen da ya haddasa ruɗani.
Shin Wike ya koma APC ko yana nan a PDP?
Amma da yake jawabi ranar Laraba da daddare, Ministan Abuja ya jaddada cewa yana nan daram a babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP.
Haka zalika ya bayyana cewa ba bu wanda ya biyo shi bashin neman tafiya saboda ya mara wa shugaba Tinubu baya a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Da aka tambaye shi ko yana tsoron jam’iyyarsa za ta dauki matakin ladabtarwa a kansa, tsohon gwamnan jihar Ribas ya amsa da cewa: “Wace jam’iyya kenan? Su waye su?"
Rabiu Kwankwaso Ya Yaba Wa Shugabannin NNPP Na Jihohi
A wani rahoton kuma Kwankwaso ya karɓi bakuncin shugabannin jam'iyyar NNPP na jihohi a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Tsohon gwamnan Kano ya yaba musu bisa abin da ya kira kokarin tabbatar da tsarukan da jam'iyyar NNPP ta zo da su.
Asali: Legit.ng