Rabiu Kwankwaso Ya Yaba Wa Shugabannin NNPP Na Jihohi Kan Abu 1

Rabiu Kwankwaso Ya Yaba Wa Shugabannin NNPP Na Jihohi Kan Abu 1

  • Rabiu Kwankwaso ya karɓi bakuncin shugabannin jam'iyyar NNPP na jihohi a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja
  • Tsohon gwamnan Kano ya yaba musu bisa abin da ya kira kokarin tabbatar da tsarukan da jam'iyyar NNPP ta zo da su
  • Wannan na zuwa ne bayan wata ƙungiya ta NNPP ta sanar da dakatar da Kwankwaso bisa zargin cin amanar jam'iyya

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yaba wa shugabannin jam'iyyar na jihohi bisa abinda ya kira riko da kyawawan tsarukan NNPP.

Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na dandalin X, wanda aka fi sani da Tuwita a baya.

Hotun Kwankwaso da shugabannin NNPP yayin da suka kai masa ziyara.
Rabiu Kwankwaso Ya Yaba Wa Shugabannin NNPP Na Jihohi Kan Abu 1 Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Ya kuma wallafa wasu Hotuna da suka nuna shugabannin NNPP na jihohi tare da jiga-jigan jam'iyyar yayin da suka kai masa ziyara a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tattara Ya Fice Daga NNPP Bayan Dakatar da Shi? Gaskiya Ta Bayyana

Jagoran NNPP na ƙasa, Kwankwaso ya rubuta a shafinsa cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Da safiyar yau ne na karbi bakuncin daukacin shugabannin jam’iyyar mu ta NNPP na jihohi tare da wasu manyan jiga-jigai a gidana da ke Abuja."
"Ina godiya da wannan ziyara, kuma ina yaba musu bisa ci gaba da kokarin da suke yi na tabbatar da tsarin jam’iyyar."

Yadda aka dakatar da Kwankwaso daga NNPP

Wannan na zuwa ne bayan wata tawaga karkashin jagorancin jiga-jigan NNPP, Boniface Aniebonam da Agbo Major, sun dakatar da Kwankwaso a wani taro na musamman da suka gudanar a Legas.

A cewarsu, shaidu sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Kano yana da hannu a wasu ayyuka na cin amanar jam'iyya a tarurruka daban-daban.

Sai dai jam’iyyar NNPP ta ce dakatarwar da aka yi wa Kwankwaso ba ta da tushe, inda ta kori wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da Dokta Boniface Aniebonam da Agbo Major wadanda suka jagoranci taron.

Kara karanta wannan

Ahaf: Wike Ya Sake Takalar Fada Tsakaninsa Da Atiku, PDP Ya Kalubalancesu Abu 1

Wani jigon NNPP a jihar Katsina, Abubakar Ahmad, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa zancen dakatar da Kwankwaso bai taso ba domin shi ya ɗaga jam'iyyar.

A cewarsa, ya yi mamaki da ya ga labarin wai NNPP ta dakatar da Kwankwaso domin idan har Madugu ya bar jam'iyyar babu wanda zai rage.

A kalamansa, jigon ya ce:

"Ni abun mamaki ya bani, wai BoT sun dakatar da Kwankwaso, to ai da cewa suka yi sun rushe jam'iyyar kawai, domin sama da kaso 80 na mambobi shi suka biyo."

Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Sabon Juyin Mulkin Sojoji a Gabon

A wani labarin kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da sabon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Gabon.

Tinubu ya nuna damuwarsa kan yadda juyin mulki ke yaɗuwa a Afirka, yana mai cewa ba zasu lamurci ci gaba da kwatar mulki da ƙarfin bindiga ba.

Kara karanta wannan

Uwar Jam’iyya Ta Fadi Matsayin Rabiu Kwankwaso a NNPP Ana Tsakiyar Rikici

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262