'NNPP Ce Ta Bai Wa Kwankwaso Izinin Ganawa da Tinubu a Faransa', Buba Galadima
- Jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi martani kan cece-kucen da ake na dakatar da Rabiu Kwankwaso
- Galadima ya ce jam’iyyar da kansu su ka bai wa Kwankwaso damar ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu
- Ya caccaki wasu daga cikin mambobin jam’iyyar inda ya ce sun yi kankanta su san Kwankwaso ya nemi izini ko sabanin haka
FCT, Abuja – Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ce ta bai wa Rabiu Musa Kwankwaso damar ganawa da Shugaba Bola Tinubu.
Galadima ya bayyana haka ne yayin hira da ‘yan jaridu a yau Laraba 30 ga watan Agusta a Abuja.
Meye Buba Galadima ke cewa game da Kwankwaso?
A ranar Talata 29 ga watan Agusta, kwamitin amintattu na jam’iyyar karkashin jagorancin Boniface Aniebonam ya dakatar da Kwankwaso kan zargin zagon kasa wa jam’iyyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma wani bangare na jam’iyyar da ke goyon bayan Kwankwaso sun yi fatali da hukuncin tare da mayar da shi jam’iyyar, TheCable ta tattaro.
Har ila yau, bangaren sun kuma dakatar da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Agbo Major, Newspeakonline ta tattaro.
Galadima ya ce da izininsu Kwankwaso ya gana da Tinubu
A cewar Buba Galadima:
“Kwankwaso ya nemi izini daga gare mu cewa zai je Faransa, mambobi 13 manya na jam'iyya su ka zauna cewa shugaban kasa ya na son ganinshi.
“Ya zo ya sanar da mu cewa shugaban kasa na son ganinshi kuma bai zai iya zuwa ba tare da neman izini ba.
“Ya dawo ya fada mana cewa shugaban kasa ya roki ya na son aiki tare da mu, lokacin da muka amince za mu yi aiki da su, zamu samu wata hanyar shawo kan lamarin.”
Galadima ya ce Agbo ba shi da girman da zai san ko Kwankwaso ya nemi izini ko bai nema ba, saboda ba ya daga cikin manyan ‘yan jam’iyya.
Buba Galadima Ya Yi Magana Kan Dakatar Da Kwankwaso A NNPP
A wani labarin, Alhaji Buba Galadima ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar NNPP a kwanakin nan.
Buba Galadima wanda yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar ya bayyana batun dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam'iyyar a matsayin wasan kwaikwayo.
Asali: Legit.ng