Zaben Imo: Gwamna Uzodinma Na Gab Da Shan Kashi, Jam'iyyar PDP

Zaben Imo: Gwamna Uzodinma Na Gab Da Shan Kashi, Jam'iyyar PDP

  • Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin cewa nan ba da jimawa ba za ta kwace mulkin jihar Imo daga hannun gwamna Hope Uzodinma
  • Kakakin PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce APC ta fahimci ba zata kai labari ba shiyasa ta koma tada hankula da rikice-rikice
  • Ya ce ba bu wani abin a zo a gani da gwamna Uzodinma ya yi wa mutanen Imo kuma sun kudiri aniyar canza shi a zaben watan Nuwamba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Imo - Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta bayyana kwarin guiwar cewa gwamna Hope Uzodinma na kan hanyar tattara komatsansa ya bar gidan gwamnatin jihar Imo.

Jam'iyar PDP ta yi iƙirarin cewa alamu sun nuna gwamna Uzodinma na kan siraɗin shan kashi duba da yadda mutane ba su jin daɗin mulkinsa da kuma gajiya da APC a Imo.

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

Jam'iyyar PDP ta ce zata kwace mulki a jihar Imo.
Zaben Imo: Gwamna Uzodinma Na Gab Da Shan Kashi, Jam'iyyar PDP Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Sakataren watsa labarai na PDP ta ƙasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

PDP ta yi tir da abubuwan da ke faruwa a Imo

Ya kuma ce PDP ta yi Allah wadai da ƙaruwar tashe-tashen hankula, kamfe mai muni da kuma farfagandar da “Gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodimma ke yi wa al’ummar jihar Imo.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton Leadership, Ologunagba ya ce:

"A zahiri gwamna Hope Uzodinma da gwamnatin APC sun fara fargabar faɗuwa zaɓe da ke tunkararsu nan kusa ganin yadda mutane suka karbi ɗan takarar mu na gwamna, Sanata Samuel Anyanwu da mataimakinsa."
"APC ta fusata da yadda al'ummar jihar Imo suka fito fili suka juya wa gwamna Uzodinma baya sabida mummunar gazawar da ya yi, ya kawo musu tsadar rayuwa da kashe-kashen fararen hula a mulkinsa."

Kara karanta wannan

Alamu Sun Nuna Abba Ya Karaya a Shari’ar Zaben Gwamna - Tsohon Hadimin Ganduje

"Bayan APC ta fahimci cewa babu yadda za a yi Gwamna Uzodimma ya samu nasara idan aka yi sahihin zaɓe cikin lumana, sai ta fara amfani da ƙarfin iko wajen yi wa ‘yan adawa zagon kasa."

Ologunagba ya ayyana cewa babu wani tashin hankali, tsokana, ko tsangwama da zai dakatar al’ummar jihar Imo daga yunkurinsu na dawo da zaman lafiya a jiharsu karƙashin PDP.

Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur, Minista

A wani labarin na daban kuma Ministan Yaɗa Labarai na Tarayya, Mohammed Malagi, ya bayyana amfanin cire tallafin fetur ga rayuwar yan Najeriya.

Bayan gana wa da gwamnan Neja, Malagi ya ce mutane zasu sha walaha a karon farko amma daɗin na nan zuwa a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262