Ganduje Ya Bukaci 'Yan Kasuwa Su Goyi Bayan Ministan FCT Nyesom Wike
- Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa buƙatarsa ga wata kungiya ta 'yan kasuwa
- Ya nemi su bai wa Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike haɗin kai wajen gyara birnin na Abuja
- Ya ba su tabbacin cewa Wike zai gyara harkokin tsaro da sufuri domin samun ingantaccen yanayi na kasuwanci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa buƙatarsa ga wata ƙungiya ta gamayyar 'yan kasuwa na Arewa.
Ya buƙaci 'yan kasuwar da su bai wa Nyesom Wike haɗin kai wajen ganin ya gyara tsarukan babban birnin tarayya Abuja ta yadda su ma za su ji daɗin gudanar da kasuwanci.
Ganduje ya yi wannan kira ne a yayin da 'yan kasuwar suka kawo ma sa ziyara a ofishinsa da ke sakatariyar APC ta ƙasa kamar yadda The Punch ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ganduje ya ce Wike zai gyara birnin tarayya
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da 'yan kasuwar, Ganduje ya bayyana Wike a matsayin jajirtaccen mutum wanda zai gyara Abuja kamar yadda ya gyara jihar Ribas.
Ganduje ya ba da tabbacin cewa Wike zai gyara tsarin tsaro da kuma harkokin sufuri na babban birnin tarayya kamar yadda The Sun ta wallafa.
Ya kuma bayyana cewa ministan zai gyara wutar lantarkin birnin ta yadda 'yan kasuwa za su samu damar gudanar da kasuwancinsu da daddare.
Ganduje ya yi sabbin naɗe-naɗe a jam'iyyar APC ta ƙasa
A wani labarin na daban kuma, kun karanta cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci rantsar da mutane shida na kwamitin ayyuka na jam'iyyar.
Taron rantsarwar ya gudana ne a babbar hedikwatar jam'iyyar da ke Babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a da ta gabata.
Jam'iyyar PDP ta zargi APC da shirya ma ta tuggu a Zamfara
Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan tuggun da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta ce ta gano jam'iyyar APC mai mulki na shirya ma ta a jihar Zamfara.
PDP ta zargi tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari Abubakar da bai wa 'yan Majalisar Dokokin jihar cin hanci domin tsige gwamnan jihar Dauda Lawal Dare.
Asali: Legit.ng