Rudani Yayin da Wike Ya Shiga Jerin Mambobin Kwamitin Kamfen APC a Bayelsa

Rudani Yayin da Wike Ya Shiga Jerin Mambobin Kwamitin Kamfen APC a Bayelsa

  • An shiga ruɗani yayin da sunan Wike ya shiga jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC a jihar Baylesa
  • A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, INEC zata gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa
  • Tun a farkon watan nan, PDP ta kaddamar da kwamitin kamfe kuma tsohon gwamnan Ribas ɗin yana ciki a matsayin mamba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ƙara haddasa ruɗani dangane da makomar siyasar ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Hakan ta faru ne yayin da aka ga sunan Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma jigon PDP, ya shiga jerin sunayen tawagar yaƙin neman zaben APC a zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Rudani Yayin da Wike Ya Shiga Jerin Mambobin Kwamitin Kamfen APC a Bayelsa Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Har yanzu dai Mista Wike bai fito ƙarara ya bayyana wa 'yan Najeriya cewa ya fice daga jam'iyyar PDP ba, sai dai fitaccen ɗan siyasan yana ɗasawa da jiga-jigan APC.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Daba Da Haɗin Kan 'Yan Sanda Sun Kai Kazamin Hari Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Ɓarna

A ranar Talatan nan da muke ciki, 29 ga watan Agusta, 2023, jam'iyyar APC ta fitar da sunayen mambobin kwamitin kamfe domin tunkarar zaben gwamnan da ke tafe a jihohi 3.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 za a fafata zaben gwamna a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa, kuma tuni jam'iyyun siyasa suka fara haramar tunkarar zaben ciki harda APC.

Jerin sunayen tawagar yaƙin neman zaɓen APC da Legit.ng Hausa ta gani, ya ƙunshi sunan ministan Abuja kuma babban jigo a jam'iyyar PDP, lamarin da ya ƙara haddasa ruɗani.

Wasu daga cikin jiga-jigan kwamitin kamfen Bayelsa

A cikin jerin sunayen, Sakataren tsare-tsaren APC na kasa, Sulaiman Muhammad Argungu, ya sanya sunan Wike da wasu manyan jiga-jigan siysasa a kwamitin kamfen Bayelsa.

Daga cikin ƙusoshin APC masu riƙe da madafun iko da suka shiga tawagar kamfen harda shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya.

Kara karanta wannan

Asari Dokubo Ya Ziyarci Shugaban APC Abdullahi Ganduje, Hotuna Da Bayanai Sun Fito

A farkon watan nan, PDP ta kaddamar da kwamitin kamfe na mutum 72 a jihar Bayelsa karkashin jagorancin gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, tare da Nyesom Wike a matsayin mamba.

Jerin Ministocin da Har Yau Shugaba Tinubu Bai Nada Ba da Dalilai

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin ma'aikatun da har kawo yanzu shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bai kai ga naɗa ministoci ba.

Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 45 ranar Litinin 21 ga watan Agusta, 2023, adadi mafi yawa a nahiyar Afirka kuma karo na farko a tarihin Najeriya tun 1999.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262