Kwamitin Amintattu Na NNPP Ya Dakatar Da Rabiu Kwankwaso Na Watanni 6

Kwamitin Amintattu Na NNPP Ya Dakatar Da Rabiu Kwankwaso Na Watanni 6

  • An dakatar da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso daga Jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari
  • Kwamitin amintattun jam'iyyar na jihar Kano ne suka fitar da wannan sanarwa a ranar Talata
  • 'Yan kwamitin sun zargi jagoran ɗariƙar kwankwasiyya da aikata laifin cin amana ga jam'iyyar

Kano - Kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari sun sanar da dakatar da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na tsawon watanni shida.

Kwamitin amintattun sun fitar da sanarwar dakatarwar ta Kwankwaso a ranar Talata, 29 ga watan Agusta kamar yadda aka wallafa a shafin TVC News.

An dakatar da Kwankwaso daga NNPP
Kwamitin amintattu ya dakatar da Rabiu Kwankwaso daga jam'iyyar NNPP. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Dalilin dakatar da Kwankwaso daga jam'iyyar NNPP

Kwamitin amintattun dai ya ce ya ɗauki wannan matakin ne a kan Rabiu Musa Kwankwaso saboda zarginsa da cin amanar jam'iyya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Kara Haddasa Ruɗani a PDP Kan Ministan Shugaba Tinubu

Tun bayan kamalla zaben 2023 ne dai jam'iyyar ta NNPP ta faɗa cikin rikici, inda ake samun zarge-zargen cin amana a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da ke riƙe da Kujerar gwamnan Kano.

Sai dai da alama rikicin ya kai maƙura, sakamakon fitowar wannan sanarwa ta dakatar da Rabiu Kwankwaso wanda shi ne ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar, kuma jagoranta na ƙasa.

Hakan ya biyo bayan dakatar da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa da aka yi a kwanakin baya, duk da cewa kwamitin amintattun bai aminta da hakan ba.

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shaguɓe kan hana shi minista

A wani labarin na daban kuma, kun karanta shaguɓen da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Kwankwaso kan hana shi minista da Tinubu ya yi.

Ganduje a cikin wani ɗan gajeren bidiyo, ya bayyana cewa Tinubu ya yi wasa da hankali Kwankwaso, saboda lura da ya yi cewa yana son zama ministan Birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar NNPP Ta Bayyana Gaskiya Dangane Da Dakatar Da Rabiu Musa Kwankwaso

Shaguɓen na Ganduje na zuwa ne bayan bayyanawa gami da rantsar da sabbin ministoci 45 da Shugaba Bola Tinubu ya yi a cikin 'yan kwanakin nan.

Kwankwaso, Abba da sauran 'yan jam'iyyar NNPP sun yi taron addu'a

Legit.ng a baya ta yi kan taron addu'a da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta shirya dangane da shari'ar zaɓe da ke gudana.

Sun yi addu'ar ne domin neman Allah ya basu nasara a shari'ar zaɓen jihar da ake yi a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng